Da duminsa: Jigon APC kuma tsohon gwamnan jihar Filato ya rasu
- Jethro Akun, tsohon mataimakin gwamnan jihar Filato ya rasu a ranar Alhamis
- Dattijon kuma jigo a jam'iyyar APC ya rasu yana da shekaru 76 a duniya bayan fama da rashin lafiya
- Ya yi mataimakin gwamnan Filato ne bayan tsige Joshua Dariye tare da maye gurbinsa da Botmang
Tsohon gwamnan jihar Filato, Jethro Akun, ya rasu yana da shekaru 76 a duniya.
Dattijon ya rasu a ranar Alhamis da safe bayan fama da yayi da gajeriyar rashin lafiya.
Kafin rasuwar shi, Akun jigo ne a jam'iyyar APC, TVC news ta ruwaito.
An nada shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Filato lokacin mulkin Michael Botmang wanda ya maye gurbin tubabben gwamna Joshua Dariye.
KU KARANTA: 'Yan bindiga suun kwashe N20m daga hannun jami'an gwamnatin Ekiti
Akun da Botmang sun kwashe watanni shida a karagar mulkin jihar Filato kafin kotun koli ta saukesu tare da bayyana shugabancin rikon kwaryan ba bisa ka'idar shari'a bane.
KU KARANTA: 2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan
A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya kushe korar da ake wa 'yan kasar nan daga wasu sassan Najeriya inda yace dan Najeriya yana da damar zabar inda yake son zama.
Tsokacinsa na zuwa ne bayan kiran da ake ta yi ga Fulani makiyaya da su bar wasu sassan kasar nan a kan rashin tsaro.
Farko daga cikin wannna bukatar ta fito ne daga gwamnatin jihar Ondo a kan cewa makiyaya su bar dajikan jihar, The Cable ta wallafa.
Amma kuma a wata takarda da El-Rufai ya fitar a ranar Laraba, ya kushe kiran da ake wa 'yan kasa da su bar wasu sassan kasar nan tare da kira ga gwamnonin jihohi da su tsaya tsayin daka domin gujewa rikici.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng