'Yan bindiga suun kwashe N20m daga hannun jami'an gwamnatin Ekiti

'Yan bindiga suun kwashe N20m daga hannun jami'an gwamnatin Ekiti

- 'Yan bindiga sun kwace N20,000,000 a hannun akawun ofishin gwamnan jihar Ekiti a ranar Laraba a wani hari da suka kai

- Sun kai musu harin ne a wuraren titin babban ofishin gwamnatin jihar dake Ado-Ekiti bayan sun ciro kudin daga banki

- Ganau sun tabbatar da yadda 'yan bindigan suka bude musu wuta a hanyarsu ta dawowa daga bankin kafin su kwace kudaden

Wasu 'yan bindiga sun kwace N20,000,000 daga hannun akawun ofishin gwamnan jihar Ekiti a ranar Laraba a wani hari da suka kai, The Nation ta wallafa.

Sun kai musu harin ne suna hanyar dawowa daga wani banki wuraren titin ofishin gwamnati dake Ado-Ekiti inda suke ciro kudaden.

Ganau sun tabbatar da yadda 'yan bindigan suka yi ta harbe-harbe kafin su kwace kudaden daga hannunsu.

'Yan bindiga suun kwashe N20m daga hannun jami'an gwamnatin Ekiti
'Yan bindiga suun kwashe N20m daga hannun jami'an gwamnatin Ekiti. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Aisha Yesufu ta yi wa Nnamdi Kanu wankin babban bargo a kan Fulani makiyaya

A cewar wani ganau, "Wasu 'yan bindiga sun budewa akawun gwamnatin jihar Ekiti wuta a hanyarsu ta komawa daga ciro kudi, 'yan bindigan sun yi musu kwanton bauna tsakanin Chicken Republic da Fujayi Park inda suka kwace dumbin dukiyar."

Sai da suka yi ta harbe-harbe a iska kafin su tsere ta wuraren GRA.

Al'amarin ya janyo cikas ga harkokin kasuwanci a jihar inda gidajen mai, kasuwanni, shaguna da wuraren cin abinci suka yi gaggawar rufewa sannan mutane suka yi ta ranta a na kare.

KU KARANTA: An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto

A wani labari na daban, duk da soyayya da Aliko Dangote, bakar fata da yafi kowa kudi a duniya, masu gidan haya a arewacin Miami da ke florida sun fatattaki Autumn Spikes sakamakon kasa biyan kudin haya na watanni shida da tayi.

Kamar yadda Premium Times ta gano, Spikes da Dangote sun yi soyayyar sirri na kusan shekaru 10 kafin daga bisani su rabu dutse a hannun riga.

Amma ko a lokacin da alakar ke nan lafiya kalau, Spikes ta tara kudin haya har $13,230 daga watan Maris zuwa Augustan 2020, takardun kotun da jaridar Premiuum Times ta gani ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: