El-Rufai ya kushe yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga wasu sassan kasar nan

El-Rufai ya kushe yadda ake fatattakar 'yan Najeriya daga wasu sassan kasar nan

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi Allah wadai da yadda ake korar 'yan kasa daga wani sassan Najeriya

- Kamar yadda ya sanar, ya dace a ce kowanne dan Najeriya yana da damar zama a kowanne sashin kasar nan

- Ya yi kira da takwarorinsa na sauran jihohi da su tsame kansu daga yadda ake kai wa 'yan wasu kabilu hari

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya kushe korar da ake wa 'yan kasar nan daga wasu sassan Najeriya inda yace dan Najeriya yana da damar zabar inda yake son zama.

Tsokacinsa na zuwa ne bayan kiran da ake ta yi ga Fulani makiyaya da su bar wasu sassan kasar nan a kan rashin tsaro.

Farko daga cikin wannna bukatar ta fito ne daga gwamnatin jihar Ondo a kan cewa makiyaya su bar dajikan jihar, The Cable ta wallafa.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An tsinto rubabbiyar gawar yariman da aka yi garkuwa da shi

El-Rufai ya kushe fatattakar Fulani da ake yi daga jihohin kudu
El-Rufai ya kushe fatattakar Fulani da ake yi daga jihohin kudu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Amma kuma a wata takarda da El-Rufai ya fitar a ranar Laraba, ya kushe kiran da ake wa 'yan kasa da su bar wasu sassan kasar nan tare da kira ga gwamnonin jihohi da su tsaya tsayin daka domin gujewa rikici.

"Gwamnatin jihar Kaduna ta ci karo da wani bidiyo mai bada takaici inda ake ganin wasu kabilu sun kashe wasu tare da kwashe musu kadarori. Wannan yana zuwa ne bayan an bai wa Fulani wa'adin barin wasu jihohi," takardar tace.

"Wasu daga cikin 'yan jihar Kaduna sun same ni inda suke tambayar ko wannan bidiyon an yi su ne sakamakon goyon bayan shugabanninsu. Na dai yi maganar a kan amfanin zaman lafiya saboda ban san ingancin wannan bidiyon ba.

“A madadin gwamnatin jihar Kaduna, ina kira ga 'yan najeriya da ke zama a jihar mu da su mutunta dokokin zama tare da kare hakkin dan Adam domin tabbatar da zaman lafiya tare da tsaro.

"Ina kira ga takwarorina da ke sauran jihohi da su fitar da makamanciyar wannan takarda tare da tsame kansu daga dukkan hare-hare da kashe-kashe."

KU KARANTA: Hoton dankareriyar motar miliyoyin naira da Emmanuella ta siya ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, wasu yara 2, Maryam Abubakar da Abdulkadir Abubakar sun rasa rayukansu bayan sun sha wani tsumi da mai maganin gargajiya ya basu.

Mahaifiyarsu, Sadiya Abubakar, yanzu haka bata san inda kanta yake ba, likitoci suna iyakar kokarin ganin sun ceto rayuwarta a asibiti.

Al'amarin ya faru ne a ranar Talata a Kwarin Barke dake Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng