2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan

2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan

- Jam'iyyar APC ta ce bata da niyyar tsayar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023

- Akwai labaran da suka bayyana akan yadda wasu gwamnonin arewa suke iyakar kokarin ganin sun tabbatar ya samu tikitin tsayawa takara

- Duk da dai shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar, Mai Mala Buni, ya ce kawai kerarren labari ne babu burbushin gaskiya a cikinsa

Jam'iyyar APC ta ce bata da shirin tsayar da tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben 2023.

Labarai sun yi ta yawo a makon da ya gabata akan yadda gwamnonin arewa suka tsaya tsayin-daka wurin tabbatar da tsohon shugaban kasan ya samu tikitin.

Sai dai shugaban kwamitin rikon kwarya, Mai Mala Buni ya ce ba gaskiya bane, Daily Trust ta wallafa.

2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan
2023: APC ta musanta rade-radin goyon bayan Goodluck Jonathan. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: An rasa rayuka 5, gidaje da shaguna sun babbake bayan kutse 'yan bindiga a Sokoto

Yayin da BBC Hausa take tattaunawa da Buni, ya ce ba gaskiya bane wannan labarin, na kanzon kurege ne.

"Na san an fara kirkirar labarin ne tun bayan mun kai masa ziyara ranar zagayowar haihuwarsa.

"Sai dai ziyarar ba ta wani abu bane, kawai mun ziyarci tsohon shugaban kasar ne," Buni yace.

Buni ya yabi Jonathan, inda yace ya cancanci a yabe shi saboda mutum ne shi mai son zaman lafiya.

KU KARANTA: Duk da rade-radin maye gurbinsa, IGP ya tarba shugaba Buhari bayan sauka Abuja daga Daura

A wani labari na daban, duk da soyayya da Aliko Dangote, bakar fata da yafi kowa kudi a duniya, masu gidan haya a arewacin Miami da ke florida sun fatattaki Autumn Spikes sakamakon kasa biyan kudin haya na watanni shida da tayi.

Kamar yadda Premium Times ta gano, Spikes da Dangote sun yi soyayyar sirri na kusan shekaru 10 kafin daga bisani su rabu dutse a hannun riga.

Amma ko a lokacin da alakar ke nan lafiya kalau, Spikes ta tara kudin haya har $13,230 daga watan Maris zuwa Augustan 2020, takardun kotun da jaridar Premiuum Times ta gani ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel