Muna shirin sayan rigakafin Korona daga China, gwamnatin Najeriya

Muna shirin sayan rigakafin Korona daga China, gwamnatin Najeriya

- Gwamnatin Najeriya ta yi tsokaci kan inda aka kwana kan lamarin siyan rigakafin COVID-19

- Tun da kungiyar lafiyar duniya ta zabge Najeriya daga cikin kasashen da zasu samu sahun farko, da alamun kasar Sin gwamnati ta nufa

- Kawo yanzu kasar Amurka, Birtaniya, Rasha da Sin suka samu nasarar kirkirar rigakafi

Gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da wasu kashen duniya domin samun rigakafin Korona nan da karshen watan Febrairu, 2021.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana hakan a hirarsa da kamfanin dillancin labarai NAN a Abuja.

Ministan ya ce Najeriya na da niyyar sayan rigakafin daga kasar Sin.

"Muna tattaunawa da kasar Sin kan rigakafin COVID-19, saboda haka muna shirin shigo da su daga Sin da kuma wasu kasashe," yace.

"Ina tunanin saboda bukatan da muke yi yanzu, zamu bukaci na Sin. Sun bamu hadin kai wajen kayan kare kai (PPE) da wasu abubuwa wajen yaki da COVID-19."

A watan Junairu 2021, ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi, ya ziyarci Najeriya inda ya tattauna da gwamnatin tarayya kan samun rigakafinsu na COVID-19.

A yanzu, rigakafin da kasar Sin ta samu nasarar yi sune CoronaVac, da kamfanin Sinovac yayi; sannan Sinopharm.

KU KARANTA: Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya

Muna shirin sayan rigakafin Korona daga China, gwamnatin Najeriya
Muna shirin sayan rigakafin Korona daga China, gwamnatin Najeriya
Source: Twitter

KU DUBA: Gwamnatin jihar Kano ta damke mabarata 500, za ta fara diban masu talla a titi

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar Lafiyan Duniya (WHO) ta fifita wasu kasashen Afrika kan Najeriya wajen aika rigakafin cutar Korona Pfizer-BioNTech.

Diraktar WHO na yankin Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce an zabge Najeriya ne bisa wasu dalilai.

Daga cikin kasashen Afrika 13 da suka bukaci rigakafin, kasar Cabo Verde, Rwanda, South Africa da Tunisia aka zabi fara turawa.

A cewar Moeti, ba karamar kalubale suka fuskanta ba wajen zaben kasashen saboda rashin isasshen rigakafin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel