Gwamnatin jihar Kano ta damke mabarata 500, za ta fara diban masu talla a titi
- Gwamnatin jihar Kano ta fara kwashe masu barece-barace kan titunanta
- Gwamnatin ta bayyana niyyar fara damke yara mata masu tallace-tallace
- A cewar kwamishanar harkokin matan jihar, an mayar da mabaratan jihohinsu na asali
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta damke mabarata 500 kan laifin saba dokan hana barace-barace a kan hanya a cikin jihar.
Kwamishanar harkokin matan jihar, Dr Zahra’u Muhammad-Umar, ta bayyana hakan yayinda ake mayar da mabaratan jihohinsu na asali jiya, Leadership ta ruwaito.
Dr Zahra'u ta ce an damke mabaratan ne a cikin birnin Kano kuma yawancinsu mata ne da yara.
"Wadanda aka kama sun hada da mata, maza da Almajirai. Yaran ba sa zuwa makaranta kuma basu da wani abincin kirki da suke ci," tace.
A cewarta, an yanke shawaran kama mabaratan ne domin kare rana gobensu da kuma zamar da Kano da Najeriya wuri mai kyau.
"Mun gano akwai halaye mara kyau cikin mabaratan. Za mu cigaba da damke su domin tsarkake titunanmu daga laifuka iri-iri," ta bayyana.
Dr Zahra'au ta bayyana cewa wata tsohuwa mai shekaru 70 da aka kama cikin na rike da Sigari da ashana.
"Ire-iren wadannan tsohuwar na iya lalata yara da al'umma gaba daya. Barace-barace na illa ga rayukan yaranmu, musamman idan aka dauki Almajirai aiki a gida," tace.
KU DUBA: Dalilai 3 da yasa kungiyar lafiyar duniya WHO ta fasa aikowa Najeriya rigakafin Korona
KU KARANTA: Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya
Ta jinjinawa gwamna Abdullahi Ganduje bisa goyon bayan da yake baiwa ma'aikatar wajen taimakawa mabaratan.
"Mun dauki sunayensu, kananan hukumominsu, lambobin wayansu kuma mun mayar da su jihohinsu, yayinda muke taimakonsu," ta kara.
Kwamishanan yace ba da dadewa ba ma'aikatar za ta fara diban masu talle a titi, musamman kananan yara mata.
A bangare guda, gwamnatin jihar Kano ta rushe makarantar da da Sheikh Abdul jabbar Nasiru Kabara ke yi wa dalibansa karatu a kusa da Jauful-Fara da ke filin mushe a Kano.
An dade ana dauki ba dadi game da filin tsakanin shaihin malamin da al'ummar unguwar ta filin mushe inda Shaikh Abdul Jabbar ke karatu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng