Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya

Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya

- Babban jami'in dan sanda ya ce yan Najeriya su daina zuwa wajen masu garkuwa da mutane don biyan kudin fansa

- Sau da dama, yan bindigan na sace wanda ya kai kudin fansa

- Ya yi jawabin ne biyo bayan kisan wani mutum da akayi duk da an biya kudin fansa

Kwamishanan yan sandan jihar Edo, Philip Aliyu Ogbadu, ya gargadi yan Najeriya kan biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa da kansu.

Yayin jawabi a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na Channels TV ranar Juma'a, kwamishanan ya bada shawaran cewa su rika sanar da yan sanda da wuri idan an sace musu mutum.

"Abinda nike janyo hankulan mutane kai shine idan irin haka ya faru, ku sanar da yan sanda maimakon zuwa biyan yan bindigan kudin fansa, ko da domin taya ku ciniku da su da kuma bibiyansu domin damkesu," yace.

Kwamishanan ya yi wannan jawabi ne biyo bayan kisan wani dan Najeriya mazauni Amurkan da masu garkuwa da mutane sukayi a Edo.

Mutumin mai suna, Dennis Abuda, ya zo gida Najeriya ne domin bikin Kirismeti amma suka sace shi yayinda yake hanyar zuwa tashar jirgin Legas.

Bayan biyansu kudin fansa, yan bindigan sun kashe shi.

Kwamishanan ya bayyana cewa ba'a sanar da yan sanda ba kafin aka kaiwa yan bindigan kusin fansa ba.

KU KARANTA: Nan da 2025, kashi 30 na motocin Najeriya da lantarki zasu rika amfani, Jelani Aliyu:

Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya
Ku daina biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa, Kwamishanan yan sanda ga yan Najeriya
Asali: Twitter

KU DUBA: Cikin hotuna: An hada mota mai amfani da lantarki ta farko a Najeriya

Mun kawo muku cewa bayan garkuwa da shi ranar 30 ga watan Janairun 2020 a jihar Edo, kwatsam aka tsinci rubabbiyar gawarsa a daji.

Wani babban jami'in tsaro ne ya tabbatar da tsintar gawar yariman, The Nation ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel