Dalilai 3 da yasa kungiyar lafiyar duniya WHO ta fasa aikowa Najeriya rigakafin Korona

Dalilai 3 da yasa kungiyar lafiyar duniya WHO ta fasa aikowa Najeriya rigakafin Korona

- Yunkurin samawa yan Najeriya rigakafin Korona ya fuskanci koma baya

- Kungiyar lafiya duniya WHO ta jinkirta kaiwa Najeriya rigakafin Pfizer/Biontech

- WHO ba ta bayyana lokacin da Najeriya za ta samu rigakafin ba

Kungiyar Lafiyan Duniya (WHO) ta fifita wasu kasashen Afrika kan Najeriya wajen aika rigakafin cutar Korona Pfizer-BioNTech.

Diraktar WHO na yankin Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce an zabge Najeriya ne bisa wasu dalilai.

Daga cikin kasashen Afrika 13 da suka bukaci rigakafin, kasar Cabo Verde, Rwanda, South Africa da Tunisia aka zabi fara turawa.

A cewar Moeti, ba karamar kalubale suka fuskanta ba wajen zaben kasashen saboda rashin isasshen rigakafin.

"Muna kyautata zaton aiki da sauran kasashen domin ganin sun samu daga baya," tace.

"Bayan haka, kimanin rigakafin Pfizer-BioNTech 320,000 aka ajiyewa kasashen Afrika hudu: Cabo Verde, Rwanda, Afrika ta kudu da Tunisiya. Za'a kai musu a watan Febrairu."

A cewarta. kasashen Afrika 13 suka bukaci rigakafin kuma an zabi 4 ne bisa:

1. Adadin wadanda cutar Korona ta kashe a kasar

2. Sabbin wadanda suke kamuwa da cutar

3. Isasshen kayan aikin iya ajiyan rigakafin (Sanyin kasa da -70 kan ma'aunin Celcius)

KU KARANTA: Cikin hotuna: An hada mota mai amfani da lantarki ta farko a Najeriya

Dalilai 3 da yasa kungiyar lafiyar duniya WHO ta fasa aikowa Najeriya rigakafin Korona
Dalilai 3 da yasa kungiyar lafiyar duniya WHO ta fasa aikowa Najeriya rigakafin Korona Credit: @MoetiTshidi
Asali: Twitter

DUBA NAN: Nan da 2025, kashi 30 na motocin Najeriya da lantarki zasu rika amfani, Jelani Aliyu

A ranar Juma'a, 05 ga watan Febrairu 2021, mutane 1,624 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Hakazalika an sallami mutane 1,190 a ranar.

Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 831 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 85 a Kaduna.

Abin takaici, mutane 9 sun rasa rayukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel