Saudiyya ta haramtawa kasashe 20 shiga kasar saboda COVID-19

Saudiyya ta haramtawa kasashe 20 shiga kasar saboda COVID-19

- Saudiyya ta haramtawa kasashe 20 shiga kasar na wucin gadi

- Kasar na daukar matakin ne a wani yunkurin dakile yaduwar cutar COVID-19

- Kashen sun hada da Birtaniya, Faransa, Amurka, Egypt, India da wasu da dama

Saudi Arabia a ranar Talata ta dakatar da shigar kasashe 20, kama daga kasashen dake makwabta da Amurka, a wani mataki na dakile cutar Coronavirus, Channels TV ta ruwaito.

Ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da "dakatarwar wucin gadi" da zata fara daga 9:00 na yammacin Laraba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya ya fitar.

Saudiyya ta haramtawa kasashe 20 shiga kasar saboda COVID-19
Saudiyya ta haramtawa kasashe 20 shiga kasar saboda COVID-19. Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Dakatarwar ta shafi makwabtan kasar kamar Egypt da United Arab Emirates idan aka fadada, Lebanon da Turkiyya.

A nahiyar Turai, dakatarwar ta hada da Birtaniya, Faransa, Jamus, Ireland, Italiya, Portugal, Sweden da Switzerland.

DUBA WANNAN: Jerin abubuwa hudu da aka haramtawa makiyaya aikatawa a Ekiti

Sauran wurare, harda Amurka, ya shafi Argentina, Brazil, Pakistan, India, Indonesia da Afirka ta Kudu.

Yan kasar Saudiyya, yan diflomasiyya da ma'aikatan lafiya da ke zuwa daga wasu kasashe, za a bari su su shiga kasar, "ta bin cikakkun matakan kariya", a cewar sanarwar.

Sanarwar na zuwa ne bayan ministan lafiyar kasar, Tawfiq Al-Rabiah ya yi gargadi a ranar Lahadi cewa za a iya sake sanya sabbin matakai idan yan kasa da mazauna basu bi matakan lafiya ba.

Saudiyya ta ruwaito cewa fiye da mutane 368,000 suka kamu da coronavirus yayin da kusan 6,400 suka mutu, adadi mafi yawa a kasashen Larabawa.

KU KARANTA: APC ta karyata jita-jitar cewa tana son tsayar da Jonathan a 2023

Adadin masu kamuwa da cutar a rana ya ragu zuwa kasa da 100 a farkon Janairu, idan aka kwatanta da 5,000 da ake samu a watan Yunin da ya gabata.

Sai dai, adadin da ake samu a rana ya ninka sau uku tun daga wannan lokacin, da rahotanni 310 da ma'aikatar lafiya ta kasar ta fitar ranar Talata.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel