Jerin abubuwa hudu da aka haramtawa makiyaya aikatawa a Ekiti
- An fara aiwatar da dokokin hana kiwo barkatai a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Nigeria
- Wannan a cewar gwamnatin jihar zai taimaka wurin hana rikici tsakanin makiyaya da manoma
- Kazalika, jihar ta kuma ce ya zama dole a yi wa makiyaya da ke jihar rajista kamar yadda wasu jihohin kudu ke yi
Batun rikicin makiyaya yana daya daga cikin abubuwan da ke janyo cece-kuce a Nigeria a yanzu. Har ta kai ga wasu gwamnatocin jihohi suna daukan matakai da suka banbanta da na gwamnatin tarayya.
Cikin jihohin akwai Ekiti wacce ta kafa dokar hana kiwo domin kare rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma tsare dukiyoyi da rayyukan al'umma, This Day ta ruwaito.
Gwamnatin, ta bakin Olabode Adetoyi, kwamishinan noma na jihar Ekiti ya jadada shirin gwamnatin na fara yi wa manoma da makiyaya rajista.
DUBA WANNAN: Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC
Hakan zai bata ikon sanin wadanda ke shige da fice a jihar a cewar gwamnatin.
A yayin da gwamnatin da fara aiwatar da dokar hana kiwon, Legit.ng ta yi nazarin wasu abubuwa da makiyaya ba za su iya yi ba a jihar a yanzu.
1. Babu kiwo cikin dare
2. An hana yaran da ba su balaga yin kiwo
3. Babu kiwo a wasu wurare da gwamnati ta killace kamar dazuka da gonaki
4. Makiyayi ba zai iya kiwo ba ba tare da rajista ba
KU KARANTA: Ban yi mamakin sauke ni daga mulki ba, Kwamishinan Borno da Zulum ya kora
Kwamishinan ya kara da cewa an tura jami'an Amokekun zuwa wasu wurare da gwamnati ke ganin za a iya samun rikici.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng