Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki

- Hukumar SUBEB a Jihar Kaduna ta sallami malaman firamare guda 65 daga aiki

- Hukumar ta ce an sallami malaman ne biyo bayan bincike tare da gano cewa an dauke su aiki ba bisa ka'ida ba

- Malaman sun fito ne daga karamar hukumar Sanga da ke Jihar Kaduna

Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki
Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki. Hoto: @thecableng
Asali: Facebook

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

DUBA WANNAN: Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Shugaban hukumar, Charles Danladi, ya sanar da korar malaman ga yan jarida a Gwantu, hedikwatar hukumar.

Danladi ya bayyana cewa an gano abubuwan da basu dace ba a albashin malaman, wanda ke ta hauhawa duk wata ba tare da daukar sabbin ma'aikata ba.

A dalili haka, aka yi korafi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sunyi alkawarin ajiye makamai bayan Gumi ya bi su garuruwansu ya musu wa'azi

Ya ce Danladi ne yayi korafin lokacin taron tattaunawa na kwamitin asusun hadin gwiwa a jihar, wanda mataimakiyar gwamna ke jagoranta, kuma aka umarci SUBEB ta binciki lamarin.

"Bayan binciken mu, mu tabbatar da an dauki malamai 65 ba bisa ka'ida ba a yankin.

"An kore su daga aiki gaba daya.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel