APC ta karyata jita-jitar cewa tana son tsayar da Jonathan a 2023

APC ta karyata jita-jitar cewa tana son tsayar da Jonathan a 2023

- Jam'iyyar APC mai mulki ta karyata rahotannin cewa tana zawarcin Goodluck Jonathan don takarar 2023

- Shugaban riko na jam'iyyar, Gwamna Mai Mala Buni ya ce wasu masu wata manufa mara kyau ne suka kirkiri labarin

- Mai Mala Buni ya ce sun kai wa Jonathan ziyara ne yayin ranar zagayowar ranar haihuwarsa a matsayinsa na dattijon kasa kuma tsohon shugaban Nigeria

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta karyata jita jitar da ake yada wa cewa za ta tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa a 2023.

Wasu rahotanni a mokon da ya gabata sun ce wasu gwamnonin APC na kokarin ganin tsohon shugaban kasar ya samu tikitin APC a 2023.

Jam'iyyar ta yi bayanin cewa wannan labarin ba gaskiya bane kawai wasu masu neman tada zaune tsaye ne suka kirkiri labarin da wata manufarsu, Vanguard ta ruwaito.

APC ta karya jita jitar cewa za ta tsayar da Jonathan a 2023
APC ta karya jita jitar cewa za ta tsayar da Jonathan a 2023. Hoto: Premium Times
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni wanda shine shugaban kwamitin riko na APC, ya shaidawa BBC Hausa cewa babu wani batun zawarci da jam'iyyar ke yi wa tsohon shugaban kasar.

"Wadanda ke yada wannan labarin, tsoro su ke yi. Amma a yanzu, babu wani batun wanda za mu tsayar takarar shugaban kasa a 2023 a APC.

"Idan ma suna la'akari da ziyarar da muka kai masa a baya bayan nan ne, mun tafi ne don taya shi murnar ranar zagayowar haihuwarsa a matsayin tsohon shugaban kasar Nigeria.

KU KARANTA: Ban yi mamakin sauke ni daga mulki ba, Kwamishinan Borno da Zulum ya kora

"Kuma idan ana maganan zaman lafiya dole mu bashi girmansa saboda yadda ya amince da kaye a 2015 don haka ya ci matsayinsa na dattijo," a cewar Buni.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164