Mai ɗaukan hotunan Aisha Buhari ya rasu

Mai ɗaukan hotunan Aisha Buhari ya rasu

- Allah ya yi wa mai daukan hoton Aisha Buhari, Mohammed Yusuf Ovajimo, rasuwa

- Direktan watsa labarai na ofishin First Lady, Suleiman Haruna ne ya sanar da rasuwar

- Ya bayyana marigayi Ovajimo a matsayin kwararre a aikinsa kuma mai kyakyawan alaka da mutane

Hajiya Aisha Buhari, mai dakin shugaba Muhamamdu Buhari ta yi rashin mai daukan ta hotuna, Mista Mohammed Yusuf Ovajimo.

Direktan watsa labarai na ofishin First Lady, Suleiman Haruna ne ya bada sanarwar rasuwar Ovajimo a shafinsa na Facebook.

Mai ɗaukan hotunan Aisha Buhari ya rasu
Mai ɗaukan hotunan Aisha Buhari ya rasu. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace

A halin yanzu babu cikaken bayani kan abinda ya yi sanadin rasuwarsa.

Haruna, ya wallafa baitukan yabo a kan marigayin da ya ce za a yi kewansa sosai.

"Yau, mun rasa Mohammed Yusuf Ovajimo, kwararren mai daukan hotuna na First Lady ta Nigeria.

KU KARANTA: Allah ya yi wa Faresa Dahiru Yahaya rasuwa a Kano

"Kwararren mai daukan hotuna ne da ya yi fice a sana'arsa ga kuma basira da iya hulda da al'umma.

"Za a yi kewarsa matuka. Allah ya jikansa da rahama. Amin." a cewar sakon.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel