Allah ya yi wa Farfesa Dahiru Yahaya rasuwa a Kano
- Allah ya yi wa fitaccen masanin tarihi, Farfesa Ɗahiru Yahaya rasuwa a jihar Kano
- Marigayin ya rasu ne a a yau Laraba a asibiti bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Ɗan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa ya kuma ce za ayi jana'izarsa a Ungogo, Kano
Shararren farfesan Tarihi dan asalin jihar Kano, Ɗahiru Yahaya ya riga mu gidan gaskiya.
Dahiru Yahaya ya rasu yana da shekaru 75 a duniya, kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Kafin rasuwarsa ya koyar a jami'ar Bayero ta Kano da jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
DUBA WANNAN: FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace
Ya rasu ne a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairun shekarar 2021 a wani asibiti bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.
Ɗan uwan marigayin malamin jami'an, Bashir Habib Yahaya, ya tabbatar wa manema labarai rasuwarsa.
Ya kuma ce za a yi wa marigayin jana'iza a gidansa da ke Ungogo a jihar Kano misalin ƙarfe 4 na yamma.
KU KARANTA: Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga ƙasashen ƙetare ne kai kai hare-hare a jiharsa
Ya ce marigayin ya rasu ya bar mata uku, yara ashirin-da-biyu da jikoki masu yawa.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng