FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace

FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace

- Gwamnatin tarayya za ta fara sayar da kadarorin da ta kwace daga wasu mutane da suka mallake su ta haramtaciyyar hanya

- Cikin kadarorin, akwai wadanda aka kwace daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Alison Diezani, tsohon babban hafson tsaro, Alex Badeh da sauransu

- Shugaban kwamitin da aka kafa domin sayar da kadarorin, Daya Apata ne ya sanar da hakan inda ya ce suna aiki tare da ofishin atoni janar da wasu hukumomin tsaro

Kwamitin da aka kafa domin sayar da kayayyakin da gwamnatin tarayya ta kwace daga masu laifi ta fara sayar da wasu kadarori 25 a sassan kasar daban-daban. Daya Apata, shugaban kwamitin ya sanar da hakan a jiya yayin taron manema labarai.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 9 ga watan Nuwamba ya kafa kwamitin bayan ganin akwai bukatar hakan sannan ya umurci ofishin atoni janar na kasa ta saka ido kan ayyukan kwamitin na karbo kadarorin gwamnati da sayar da su, Vanguard ta ruwaito.

FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace
FG ta fara sayar da gwala-gwalen Diezani, gidajen Badeh da wasu kayayyakin da ta kwace. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ban yi mamakin sauke ni daga mulki ba, Kwamishinan Borno da Zulum ya kora

Apata ya ce kwato kadarorin gwamnati da sayar da su na cikin ayyukan shari'a.

Ya ce kwamitin yana da wakilai daga hukumomin tsaro da suka hada da, Yan sanda, Sojojin Ruwa, EFCC, ICPC da ma'aikatun kudi, shari'a, ayyuka da sauransu.

Cikin kadarorin da za a sayar akwai filaye, masana'antu, injina, motoccin hawa, kayan ado kamar gwala-gwalai da sauransu.

Duk da cewa sanarwar ba ta fayyace kadarorin da za ayi gwanjon su ba, EFCC a baya ta samu izini daga kotu na fara sayar da wasu kadarorin da ta kwace daga hannun tsohuwar ministan man fetur, Alison Diezani Madueke.

DUBA WANNAN: Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga ƙasashen ƙetare ne kai kai hare-hare a jiharsa

A 2019, kotun tarayya a Legas ta bada umurnin kwace gwala-gwalai na Diezani da kudinsu ya kai Dalla miliyan 40. Duk dai a shekarar, kotu ta kwace kimanin Naira biliyan 12.2 mallakar Patience Jonathan tsohuwar matar shugaban kasa Goodluck Jonathan.

An kuma kwace wani asibiti (Dews Hope Hospital, a Owerri) na N1.5 biliyan da aka alakanta da hadimin tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Bayan taron, kwamitin ta ziyarci wasu wurare hudu a Abuja ciki har da gida mai lamba 14 Adzope Crescent Wuse 2 Abuja da aka kwace daga tsohon babban hafson sojojin sama daga bisani babban hafson tsaro, Alex Badeh.

Kwamitin ta kuma ziyarci wasu wurare a birnin na Abuja da duk za a sayar da su.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel