A bari mutane su mallaki bindiga AK47 tun da an gaza kare su, Gwamnan Taraba ga Buhari

A bari mutane su mallaki bindiga AK47 tun da an gaza kare su, Gwamnan Taraba ga Buhari

- An jana'izar shugaban karamar hukumar da yan bindiga suka kashe a jihar Taraba

- Gwamnan jihar ya yi alhinin mutuwar shugaban karamar hukumar

- Ya bukaci Buhari ya bari mutane su mallaki bindiga don kare kansu

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya bukaci gwamnatin tarayya ta bari mutane su mallaki bindigogin kansu dmin kare kansu da iyalansu saboda yadda matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Channel TV ta ruwaito cewa gwamna Ishaku ya bayyana haka ne ranar Talata yayinda shugabannin kananan hukumomin jihar suka ziyarceshi bayan jana'izar daya daga cikinsu da yan bindiga suka kashe.

Gwamnan ya yi alhinin tsanantan rashin tsaro, inda Najeriya bata taba shiga irin wannan halin ba.

"Matsalar tsaro a kasar nan tayi munin da bata taba yi ba kuma ya zama wajibi mu tashi tsaye. Mu a matsayin shugabanni mun bada shawarin mu domin kawo sauyi, ba zai yiwu ku cigaba da abu daya kuma ku saurari wani sakamako daban ba," yace.

"Idan mun gaza baiwa al'ummarmu tsaro, mu bari su mallaki AK-47, saboda idan kowa na da lasisin AK-47, na rantse babu wanda zai zo gidanka."

Gwamna Ishaki ya jajantawa iyalan wadanda sua rasa rayukansu musamman iyalan shugaban karamar hukumar Ardo-Kola, Salihu Dovo, da aka kashe.

KU KARANTA: Za'a yi amfani da jirage masu sarrafa kansu wajen raba magunguna a Kaduna

A bari mutane su mallaki bindiga AK47 tun da an gaza kare su, Gwamnan Taraba ga Buhari
A bari mutane su mallaki bindiga AK47 tun da an gaza kare su, Gwamnan Taraba ga Buhari Credit: @tarabagovt
Asali: Twitter

KU DUBA: Jerin abubuwa hudu da aka haramtawa makiyaya aikatawa a Ekiti

A bangare guda, kungiyar kare hakkin Yarbawa a Najeriya, Afenifere, ta caccaki dattawan Arewa kan kiran da sukayi ga Fulani Makiyaya su koma Arewa idan aka cigaba da tsangwamarsu.

Kungiyar Afenifere ta bayyana cewa babu abinda kasar Yarabawa zata ragu da shi idan Fulani suka yanke shawaran komawa Arewa, rahoton Vanguard.

Kakakin kungiyar, Yinka Odumakin, ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel