Ba abinda zamu ragu da shi idan Fulani suka koma garinsu, kungiyar Afenifere

Ba abinda zamu ragu da shi idan Fulani suka koma garinsu, kungiyar Afenifere

- Kungiyar dattawa Arewa ta yi kira ga Fulanu Makiyaya su koma gida Arewacin Najeriya daga Kudu

- Kungiyar Afenifere ta yiwa dattawan Arewa raddi kan wannan shawaran

Kungiyar kare hakkin Yarbawa a Najeriya, Afenifere, ta caccaki dattawan Arewa kan kiran da sukayi ga Fulani Makiyaya su koma Arewa idan aka cigaba da tsangwamarsu.

Kungiyar Afenifere ta bayyana cewa babu abinda kasar Yarabawa zata ragu da shi idan Fulani suka yanke shawaran komawa Arewa, rahoton Vanguard.

Kakakin kungiyar, Yinka Odumakin, ya bayyana hakan a ranar Laraba.

"Buhari ya nuna rashin damuwarsa da yan kudun da ake ciwa mutunci a kasarsu. Amma za ya cigaba abinda ya ga dama wajen kare Fulani. Babu wanda zai yi wani rashin idan makasan suka yanke shawaran komawa Futa Jalon," Odumakin ya bayyana.

DUBA NAN: Za'a yi amfani da jirage masu sarrafa kansu wajen raba magunguna a Kaduna

Ba abinda zamu ragu da shi idan Fulani suka koma garinsu, kungiyar Afenifere
Ba abinda zamu ragu da shi idan Fulani suka koma garinsu, kungiyar Afenifere
Source: UGC

KU KARANTA: Za'a yi amfani da jirage masu sarrafa kansu wajen raba magunguna a Kaduna

Kungiyar Makiyayan Arewa (NEF) ta bayyanawa al'ummar Fulani dake kudancin Najeriya su dawo gida idan ana koransu daga inda suka zaune.

Hakazalika Kungiyar NEF ta yi kiraga gwamnonin Arewa su shirya karban Fulanin dake shirin dawowa gida daga kudu.

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa wannan na kunshe cikin jawabind da kakakin kungiyar dattawan, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya saki.

Wani sashen jawabin yace: "Idan mutanen wani sashe a kasar nan sun lashi takobin koran Fulani daga yankunansu, kungiyar na bada shawara kawai su koma Arewa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel