Za'a yi amfani da jirage masu sarrafa kansu wajen raba magunguna a Kaduna
- Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa zata yi amfani da jirage masu na'ura da ke sarrafa kansu domin raga magunguna
- A sanarwar da ta fito ranar Laraba, gwamnatin jihar Kaduna ta ce zata yi amfani da jiragen wajen raba alluran rigakafi da sauran kayan tallafi
- A cewar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, gwamnatinsa ta kulla yarjejeniya da wani kamfani Amurka domin samun nasarar hakan
Gwamnatin jihar Kaduna ta kulla yarjejeniya da wani kamfanin Amurka mai suna 'Zipline' wanda ke aikin rarraba kayayyaki ta hanyar jirgi maras matuki, domin rarraba magunguna da sauran kayan kiwon lafiya a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, gwamnatin jihar ta ce za ayi amfani da jirage marasa matuka ne domin rarraba allurorin riga-kafi, kayan jini da kuma magungunan ceton rai.
A cewar Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, wannan hadakar za ta taimaka wajen tabbatar da cewa kowanne dan jihar Kaduna ya samu kulawar lafiya kamar yadda ya kamata, kamar yadda TheCable ya rawaito.
Sanarwar ta yi nuni da cewa za a rinƙa gudanar da rabon kayan ne na tsawon awanni 24 a kowacce rana, kuma za a rinƙa tura kayan daga cibiyoyi uku, inda kowacce cibiya za ta samu jirage 30 domin gudanar da aikin.
"Idan aka hada su, duka cibiyoyin rarraba kayan 3 za su tunkari rarraba akalla ton shida na kayan magunguna, a wuraren da suka haura kilomita 60,000," a cewar sanarwar.
"Wannan sabuwar kimiyya, wacce ake sa ran za ta fara aiki a zango na biyu na shekarar 2021, na daga cikin namijin kokarin gwamnatin jihar Kaduna na rarraba kayayyakin kiwon lafiya ta hanyar amfani da jirage marasa matuka, wanda zai taimaka wajen kare rayukan sama da mutane miliyan takwas, daga nan har shekaru masu yawa.
KARANTA: Na barku da Allah akan zargin da kuke min; Obasanjo ya bayar da tarihi akan marigayi Yar'adua
"Kari kan kudirin fadada rarraba kayayyakin kiwon Lafiya musamman na gaggawa, shirin rarraba kayan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka zai fadada raba allurar riga-kafin COVID-19, musamman zuwa ga ƙauyuka da karkara.
"Kamfanin Zipline ya ƙera jirage marasa matuka da ke da karfin adana kankara ko sanyi da za a iya raba allurorin riga-kafi musamman ma na cutar Covid-19 da sauran magunguna masu matukar muhimmanci."
El-Rufai ya kara da cewa gwamnatin jihar ta daga darajar cibiyoyin kiwon lafiya guda 255 domin wadatar da harkokin kula da kiwon lafiyar al'umma a jihar baki daya.
A baya bayan nan ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan dokar kariya daga cutar coronavirus da ke tilasta amfani da takunkumin fuska.
Dokar ta tanadi tara ko daurin wata shida ko gaba daya biyun ga duk wanda ya karya dokar.
Amma a karshen mako, an ga shugaban kasar yana tattaunawa da wasu gwamnonin APC a wajen sabunta rajistar sa ta jam'iyyar APC a Daura ba tare da sanya tukunkumin ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng