Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya samu waraka daga cutar Coronavirus

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya samu waraka daga cutar Coronavirus

- Bayan mako guda, gwamnan jihar Benue ya warke daga cutar Korona

- Shine gwamna na 11 da ya samu waraka daga cutar bayan kamuwa

- Gwmantin tarayya tana barazanar kafa dokar kulle a wasu jihohi biyar

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba ya sanar da cewa ya samu waraka daga cutar Korona bayan kwanaki bakwai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a Makurdi, babbar birnin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Ya mika godiyarsa da al'ummar jihar, abokansa, masoyansu a fadin tarayya bisa addu'o'insu lokacin da yake killace.

Gwamnan wanda ya koma bakin aiki ya mika godiyarsa ga mataimakin gwamna, Benson Abouno, wanda ya maye gurbinsa lokacin da yake killace.

Ortom ya yi kira ga mutan jihar su bi dokokin kariya daga cutar COVID-19.

KU DUBA: 'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya samu waraka aga cutar Coronavirus
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya samu waraka aga cutar Coronavirus Credit: @GovSamuelOrtom
Source: Twitter

KU DUBA: Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m

Mun kawo muku cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya shiga jerin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar Coronavirus.

Sakataren yada labaran gwamnan, Terver Akase, ya sanar da hakan ranar Laraba.

Akase, a jawabin da ya baiwa manema labarai a Makurdi, yace: "Sakamakon karshe na gwamna Ortom ya nuna cewa ya kamu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel