'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

- Wasu 'yan fasa kwabrin shinkafa a kan hanyar Abeokuta zuwa jihar Legas sun farmaki jami'an kwastam

- 'Yan fasan kwabrin sun jikkata wasu jami'an kwastam tare da wani sojan Najeriya

- Rundunar kwastam din sun samu nasarar kwace mota cike da shinkafar fasa kwabri

Wasu ‘yan daba da ake zargin 'yan fasa-kwabri ne a ranar Talata sun kai hari tare da raunata wasu jami’ai uku na Hukumar Kula da Ayyukan Tarayya (FOU), Zone A na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NSC) da kuma wani jami’in soja a Legas, The Nation ta ruwaito.

Jami'an, binciken ya nuna cewa, suna kan aikin sintiri ne a kan babban titin Legas zuwa Abeokuta kafin a far musu tare da ji musu rauni.

Wani kakakin kwastam, Theophilus Duniya ya fada a cikin wata sanarwa cewa jami’an Kwastam su uku da wani jami’in soja da ke aiki a cikin tawagar ‘yan sintirin sun samu raunuka daga harbin bindiga.

Ya ce jami'an sun damke motoci shida makare da shinkafar fasa kwabri kafin maharan su far musu.

KU KARANTA: Kwalejin kimiyya da fasaha na Adamawa za ta fara karatun digiri, in ji Rector

'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja
'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja Hoto: Ships & Ports
Source: UGC

Ya ce, "Wasu jami'an sashin kula da ayyukan kwastam na Tarayya sashin 'A' na Hukumar Kwastam ta Najeriya, sun gamu da farmaki daga wasu 'yan daba da ke aiki tare da masu fasa kwauri."

“Da misalin karfe 6 na ranar Talata 2 ga Fabrairu, 2021.

"Jami’an sashin, yayin da suke gudanar da aikinsu na doka na tabbatar da dokokin hana fasa-kwabri; sun yi aiki a kan bayanan sirri sannan sun kame motoci shida makare da shinkafar da aka shigo da ita ta ketare a titin Abeokuta.

An bayyana cewa, yayin da jami'an kwatsam din suka tare su, wasu 'yan bindiga da ke aiki tare da su sun farmakesu sun bude musu wuta don samun damar kwace shinkafar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga guda shida sanye da abin rufe fuska da kuma bakaken kaya sun mamaye Warsa Piti, a Gundumar Mariri da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna suka kashe mutane biyu a ranar Litinin, The Punch ta ruwaito.

An ce 'yan bindigar sun yi harbi ba kakkautawa, inda suka kashe mutanen kauyen biyu kafin su tsere zuwa cikin dajin lokacin da jami'an soji suka isa yankin.

Kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwan haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel