Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya kamu da cutar Korona
- Gwamnan Najeriya na 11 ya kamu da cutar Korona
- Watan gobe Korona za ta cika shekara daya da bulla a Najeriya
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya shiga jerin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar Coronavirus.
Sakataren yada labaran gwamnan, Terver Akase, ya sanar da hakan ranar Laraba.
Akase, a jawabin da baiwa manema labarai a Makurdi, yace: "Sakamakon karshe na gwamna Ortom ya nuna cewa ya kamu."
"Wannan ya biyo bayan sakamakon gwajin yawancin hadiman gwamnan na kusa a makonnin baya kuma aka tabbatar sun kamu."
"Duk da cewa babu alamun cutar a cikin gwamnan, ya fara jinya kamar yadda likitocinsa suka bada shawara."
A bangare guda, kasar Sin ta fara yiwa al'ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi basa sakamako na kwarai, Daily Mail ta ruwaito.
Domin yin wannan gwaji, ana bukatar tura audugar cikin dubura na tsawon inci daya zuwa biyu kuma a juyashi.
Bayan yin haka sau biyu, za'a cire audugar sannan ayi gwaji.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng