Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m

Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m

- Rahoton da Babban Bankin Duniya ya sake shiga yanayin talaucin da ciki yanzu ba tun shekarun 1980

- Rahoton yace akalla mutane kusan miliyan 20 ne zasu karu a adadin masu fama da talauci

- Rahoton hakazalika ya danganta wannan ci baya da tasirin COVI-19 a shekarar da ta gabata

Wata jami’a a Babban Bankin Duniya bangaren Tattalin Arziki mai suna Gloria Joseph Raji ta bayyana wa duniya cewa annobar cutar COVID-19 nakasa tattalin arzikin Najeriya.

Najeriya a halin yanzu na fuskantar mummunan yanayi na tallalin arziki da ba ta jima bata fuskanta ba tun shekarar 1980, in ji jaridar Punch.

“Don haka, ganin babu ci gaba a fannin tattalin arzikin ga rashin aikin yi sannan ga hauhawar farashi, mun yi kiyasin cewa adadin mutanen da ke fama da talauci zai karu da kusan mutum miliyan 15 zuwa 20 zuwa shekarar 2022.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa

Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m
Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai karu zuwa sama da 15m Hoto: Brand Communicator
Asali: UGC

"A baya mutum miliyan 83 ke fama da talauci a Najeriya a kiyasinmu na 2019,” a cewar jami'ar.

A cewarta, Najeriya na bukatar gyara da inganta manufofinta don taimakawa sana’o’i sannan a inganta walwalar 'yan ƙasar da fidda su daga kangi.

Shi ma Dakta Doyin Salami, Shugaban majalisar da ke bai wa shugaban kasar Najeriya shawara kan tattalin arziki ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta kaddamar da sauye-sauye masu yawa don fitar da 'yan kasar daga halin da suke ciki na matsanancin talauci.

Misis Raji ta ce binciken Babban Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya tana cikin wani mataki mai wuyar tsallakewa a yanzu saboda fitar da mutum miliyan sama da 100 daga cikin talauci zuwa shekarar 2030 abu ne mai wahala a gareta.

Babban Bankin ya yi la'akari da ganin cewa ko kafin annobar COVID-19, kasar na cikin wani mummunan hali.

KU KARANTA: 'Yan fasa kwabrin shinkafar waje sun jikkata wasu jami'an Kwastam da wani soja

A wani labarin, Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar, The Guardian ta ruwaito.

Matan sun yi magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin a Kaduna a wurin da ake rabon kudin.

Ya ce mutanen da ba a san su ba suna karbar kudade daga wasu daga cikin wadanda suka amfana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel