Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga ƙasashen ƙetare ne ke kai hare-hare a jiharsa

Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga ƙasashen ƙetare ne ke kai hare-hare a jiharsa

- Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya ce makiyaya Fulani da ke shigowa daga kasahen waje ne ke aikata laifuka a jiharsa

- Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da shugaban hukumar Immigration na yankin, ta kai masa ziyara a ofishinsa

- Gwamnan ya nuna damuwarsa kan adadin mutanen da ke kwararowa cikin kasar ba bisa ka'ida ba ya kuma bukaci hukumar ta NIS, ta hada kai da Amotekun

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu ya ce makiyaya daga kasashen ketare da ke zaune a dazukan jihar ne suka aikata laifuka da kai hare hare, The Punch ta ruwaito.

Akeredolu ya ce da dama cikin makiyayan da suka zo daga kasashen ketaren zaman dindindin suke yi a dazukan gwamnatin jihar kafin a bada umurnin korarsu.

Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga kasashen ketare ne kai kai hare hare a jiharsa
Gwamnan Ondo ya ce makiyaya daga kasashen ketare ne kai kai hare hare a jiharsa. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin ziyarar ban girma a ofishinsa da shugaban yankin na Hukumar Shige da Fice na Kasa, Dora Amahian, da ke wakiltan jihohin Oyo, Ondo, Osun da Ekiti ta kai masa.

Akeredolu, wanda ya bukaci jami'an hukumar su kara jajircewa domin kiyayye iyakokin jihar ya ce adadin bakin da ke shigowa jihar daga kasashen waje abin duba wa ne.

"Zai yi wu Fulani ne amma ba yan Nigeria bane. Ina ganin ya kamata a rika hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro. Hakan zai inganta aiki da samun sakamako. Ku hada kai da hukumar tsaro kamar Amotekun," a cewar gwamnan cikin jawabinsa.

Tunda farko, Misis Dora Amahian ta mika godiyarta ga gwamnan saboda kyakyawar alakar da ke tsakaninsa da hukumar ta Immigration inda ta ce himmarsa na samar da mulki na gari da romon demokradiyya ne ke samar da zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164