Ban yi mamakin sauke ni daga mulki ba, Kwamishinan Borno da Zulum ya kora
- Kwamishinan da Gwamna Zulum na jihar Borno ya tsige ya yi magana game da rasa aikinsa
- Dakta Salisu Kwaya-Bura ya ce bai yi mamakin sauke shi daga mukaminsa ba dama tunda ba shi ya nada kansa ba
- Ya kuma ce cire shi da aka yi bai da alaka da siyasa ko rawar da ya taka a tawagar annobar korona ta jihar
Tsohon kwamishinan lafiya na jihar Borno, Dakta Salisu Kwaya-Bura da ake sauke a ranar Talata ya ce sauke shi bai da alaka da siyasa, The Punch ta ruwaito.
Mai bawa gwamnan shawara na musamman kan hulda da al'umma da tsare-tsare, Malam Isa Gusau ne ya sanar da korar Kwaya-Bura tunda farko cikin wata sanarwa.
Wani sashi na sanarwar ya ce, "Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum ya sallami kwamishinan lafiya, Dakta Salihu Kwayabura daga aiki."
Gusau ya ce an dauki matakin ne domin sake yi wa ma'aikatar lafiyar alkibla sannan ya sanar da Farfesa Isa Marte a matsayin wanda zai maye gurbin Kwaya-Bura.
Kwaya-Bura, a yayin zantawar da ya yi da manema labarai daga bisani ya ce,"Ba kamar yadda wasu ke zato ba, sallama ta daga aiki bai da alaka da siyasa.
"Abin bai ba ni mamaki ba tunda ba ni na nada kai na ba tunda farko kuma na san cewa gwamnan na iya nada wani ba ni ba a lokacin da ya ke so.
"Ban yi imanin cewa siyasa ce ko wani abu mai alaka da rawar da na taka a tawagar COVID-19 ne dalilin don ni kwararren ma'aikacin lafiya ne kuma zan cigaba da bada gudunmawa a bagaren lafiya a jihar Borno," ya kara da cewa.
Asali: Legit.ng