Gwamnatin Amurka na neman Malaman Hausa da Yarbanci a jami'o'inta

Gwamnatin Amurka na neman Malaman Hausa da Yarbanci a jami'o'inta

- Amurka ne neman malaman Hausa a makarantun sakandarenta da jami'o'inta

- Wadanda suka samu nasarar shiga zasu tafi Amurka

- An bada watanni biyar ga duk wanda ke da niyyar neman aikin

Ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya tana kira ga yan Najeriya gurbin aikin karantar da yan kasar Amurka harshen Hausa da Yarbanci a kwaleji da jami'o'inta.

A sanarwan da ofishin jakadancin tayi a shafinta na yanar gizo, masu niyya zasu iya neman aikin daga ranar 1 ga Febrairu zuwa 1 ga Yuni

Jawabin ya kara da cewa wadanda ke da Digiri a harshen Turanci, Hausa, Yarbanci, zasu iya nema.

"An shirya shirin FLTA ne domin taimakawa malaman kasashen wajen gurbin aikin karantar harshen Yarbanci da al'ada ga daliban Amurka a makarantun sakandare da jami'o'i," wani sashen jawbin yace.

"Shirin na baiwa mutane daman inganta ilmin karantarwansu, kara musu ilmin harshen Turanci da kuma fadada ilminsu kan al'adun Amurka."

An fahimci cewa wadanda suka samu nasaran samun aikin daga karshe za'a dauki nauyin kudin jirginsu zuwa Amurka, kudin gida, kudin albashi, inshoran kiwon lafiya da kuma daukan nauyin karatunsu.

Za ku iya shiga nan domin karanta abubuwan da ake bukata

KU KARANTA: Cikin hotuna: Iyaye mata na gudanar da zanga-zanga, sunce a kori Fulani daga Edo

Gwamnatin Amurka na neman Malaman Hausa da Yarbanci a jami'o'inta
Gwamnatin Amurka na neman Malaman Hausa da Yarbanci a jami'o'inta Credit: lifestyle.thecable.ng
Source: UGC

DUBA NAN: Gwamnatin Kebbi ta dauki Malaman addini don yiwa Fulani wa'azi

A bangare guda, kasar Amurka ta bayar da gudummawar wani katafaren asibitin da zai taimakawa Najeriya wajen killace masu COVID-19, HumAngle ta ruwaito.

An bayar da gudummawar wurin ga Ma'aikatar Lafiya daga Ofishin Tsaro na Amurka reshen Afrika, tare da tallafin USAID, Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) da Walter Reed Army Institute of Research (WRAIR).

Mary Beth Leonard, Jakadiyar Amurka a Najeriya, tare da Olorunnimbe Mamora, karamin Ministan Lafiya, sun bude asibitin a ranar 22 ga Janairu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja, in ji Ofishin Jakadancin na Amurka a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel