Gwamnatin Kebbi ta dauki Malaman addini don yiwa Fulani wa'azi

Gwamnatin Kebbi ta dauki Malaman addini don yiwa Fulani wa'azi

- Gwamnatin jihar Kebbi ta bi sahun Zamfara da Kaduna wajen yiwa makiyaya wa'azi

- A cewar Malaman da aka dauka wannan aiki, jihilci na cikin abubuwan da haddasa ta'addanci

Gwamnatin jihar Kebbi ta samar da sabon salon yaki da yan bindiga da sace-sacen mutane a jihar musamman Fulani Makiyaya.

An kafa kwamitin Malamai masu wa'azi 65 yawanci wadanda suke jin yaren Fulani domin fadakar da makiyaya kan illan barandanci da wasu laifuka.

Wannan sabon salo ne da aka dauka domin ilmantar da makiyaya kan haramcin aikata laifuka a addinin Musulunci.

Jaridar Caliphate Trust ta ruwaito shugaban kwamitin, Asheikh Abdullahi Mamman Sheme, da cewa bayan tattaunawan da sukayi, sun gano cewa bayan amfani da kwayoyi da barasa, rashin ilimin addini na taka rawa wajen aikata laifukan da makiyaya ke yi.

Asheikh Sheme, wanda shine Moddibon Gwandu, ya ce za'a gudanar da shirin wa'azin ne sashe-sashe.

A cewarsa, za'a yi watanni uku ana wa'azi a sashe na farko yayinda za'a yi sashe na biyu bayan azumin watan Ramadan.

KU KARANTA: Abia: Muna biyan N100K kan duk wata saniya da aka kashewa makiyaya

Gwamnatin Kebbi ta dauki Malaman addini don yiwa Fulani wa'azi
Gwamnatin Kebbi ta dauki Malaman addini don yiwa Fulani wa'azi Credit: @KBStGovt
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya umarci IG Adamu ya mika takardar ritayarsa

Ya kara da cewa za'a fara wa'azin ne muddin kwamitin ta kammala tattaunawa da Ardo (shugabannin Fulani) wanda zai taimaka musu wajen sanin garuruwan Fulanin da za'a iya ziyarta.

Ya ce mambobin kwamitin sun hada da Malamai daga yaruka daban-daban a jihar.

"Yawancin mambobin kwmaitin Malaman masu yaren Fulfulde ne. An zabesu ne domin iya tattaunawa sosai tunda wadanda ake shirin yiwa wa'azi Fulani ne," yace.

"Bayan kowani wata uku, kwamitin za ta rika duba irin tasirin da wa'azin ke yi."

A bangare guda, Okezie Ikpeazu, gwamnan Abia, ya ce gwamnatin jihar na biyan makiyaya N100,000 kan kowace saniya da aka kashe sakamakon rikici tsakanin su da manoma.

Gwamnatin jihar a ranar Talata ta zargi makiyaya da sace ‘yan asalin jihar tare da lalata filayen noma tare da tura shanu cikin gonakai suna kiwo a bayyane.

Da yake magana a ranar Laraba a gidan talabijin na Channels Television na Sunrise Daily, Ikpeazu ya ce ana biyan irin wannan kudin ga manoma wadanda shanu suka bata gonakinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel