Amurka ta ginawa Najeriya asibiti mai darajar $1.3m don kebe masu COVID-19

Amurka ta ginawa Najeriya asibiti mai darajar $1.3m don kebe masu COVID-19

- Kasar Amurka ta tallafawa Najeriya da ginin wani katafaren asibitin kebe masu Korona

- Kasar ta bayyana ci gaba da hadin kanta da Najeriya wajen yaki da Korona

- Hukumar lafiya ta Najeriya tare da jakadiyar Amurka a Najeriya sun bude asibitin a Abuja

Kasar Amurka ta bayar da gudummawar wani katafaren asibitin da zai taimakawa Najeriya wajen killace masu COVID-19, HumAngle ta ruwaito.

An bayar da gudummawar wurin ga Ma'aikatar Lafiya daga Ofishin Tsaro na Amurka reshen Afrika, tare da tallafin USAID, Cibiyar Kula da Cututtuka (CDC) da Walter Reed Army Institute of Research (WRAIR).

Mary Beth Leonard, Jakadiyar Amurka a Najeriya, tare da Olorunnimbe Mamora, karamin Ministan Lafiya, sun bude asibitin a ranar 22 ga Janairu a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Jabi, Abuja, in ji Ofishin Jakadancin na Amurka a ranar Litinin.

KU KARANTA: Kadarorin da aka kona min sun kai miliyan N50m, in ji Sunday Igboho

Amurka ta ginawa Najeriya asibiti mai darajar $1.3m don yaki da COVID-19
Amurka ta ginawa Najeriya asibiti mai darajar $1.3m don yaki da COVID-19 Hoto: HumAngle
Asali: UGC

An bayyana cewa asibitin zai iya daukar mutane 40 da za a kebe.

Leonard ta bayyana gudummawar dala miliyan 1.3 na asibiti a matsayin alamar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka.

Leonard ta kuma bayyana cewa gwamnatin Amurka na nan kan bakanta na tsayawa tare da Najeriya don tabbatar da cewa ana ci gaba da bunkasa kwarewa domin ba kasar damar inganta ci gaba da kulawa da kebe masu COVID-19.

Ta kara da cewa "Tallafawa ma'aikatan kiwon lafiya wadanda ke kula da marassa lafiya a wannan cibiya da kuma duk fadin kasar, yana da matukar muhimmanci ga kokarin Najeriya na rage yaduwar COVID-19," in ji ta.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta yi barazanar rufe sansanonin NYSC a jihohi idan…

A wani labarin, Likitocin lafiya uku sun mutu yayin da wasu 53 suka kamu da kwayar ta COVID-19 tun bayan bullar kwayar cutar a jihar Kano, in ji Dakta Usman Ali, shugaban kungiyar likitocin Nijeriya (NMA), Daily Trust ta ruwaito.

Usman a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce mutuwar ta kwanan nan ta wani kwararrun masanan cututtukan da suka mutu a wata cibiyar keɓewa a ranar Litinin a makon da ya gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel