An kama matafiyi da hodar ibliss kunshe cikin riguna 68 a filin tashin jirage

An kama matafiyi da hodar ibliss kunshe cikin riguna 68 a filin tashin jirage

- Hukumar yaki da masu safarar muggan kwayoyi, NDLEA ta kama wani da hodar Iblis a cikin riguna 68 a filin tashin jirage

- Wanda aka kama, Ukaegbu Bright Onyekachi, ya ce wani Kingsley mazaunin Brazil ne ya bashi rigunan amma bai san da kwaya a ciki ba

- Hukumar ta ce masu safarar sunyi dabar sosai wurin boye kwayoyin amma jami'anta suma kwararru ne hakan yasa suka gano

Jami'an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta Nigeria, NDLEA, sun kama wani matafiyi a filin tashin jiragen sama dauke da hidar iblis mai nauyin kilo 3.3 a kunshe cikin addon da ake saka wa riguna guda 68.

An kama Ukaegbu Bright Onyekachi da ya shigo jirgi daga Sao Paolo, Brazil ta Addis Ababa a Ethiopia a filin tashi jirage na Murtala Mohammed a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

An kama matafiyi da hodar ibliss kunshe cikin riguna 68
An kama matafiyi da hodar ibliss kunshe cikin riguna 68. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC

Hakan na zuwa ne bayan kwanaki bakwai da aka kama wani hodar iblis din da kudinsa ya kai Naira biliyan 7 a filin tashin jiragen.

Sai dai Ukaegbu ya yi ikirarin cewa bai san an boye muggan kwayoyin ba a cikin kayansa inda ya ce wani Kingsley, dan Nigeria mazaunin Brazil da suka hadu sau biyu ne ya bashi kayan.

A bangarensa, kwamandan na NDLEA, Ahmadu Garba ya yi bayanin cewa wanda ake zargin ya boye muggan kwayoyin a cikin rigunan 68 ne a masanaanta da can Brazil.

A cewarsa, an yi basira sosai wurin boye muggan kwayoyin. Sai dai ya ce hukumar za ta cigaba da cin galaba a kan masu safarar miyagun kwayoyin.

KU KARANTA: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Ya ce, "Jimillar nauyin kwayoyin ya kai 3.30kg. Ba wani babban kamu bane idan ka kwantanta da 8.5kg da aka kama a baya bayan nan amma idan ka duba yadda suka boye shi abin akwai sarkakiya ciki. Jami'an mu kwararru ne shi yasa suka gano wannan.

"Suna samun kazamin kudi da safarar miyagun kwayoyi, duk abinda akwai kudi, mutane za su yi. Ina ganin Covid 19 ya dakatar da abubuwa a 2020 amma ina ganin yanzu suna son su cigaba ne."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel