Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC

Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC

- Kwamared Eradiri, tsohon kwamishinan cigaban matasa da magoya bayansa 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC

- Karamin ministan albarkatun man fetur, Timpre Sylva ne ya tarbi Eradiri da magoya bayansa a sakatariyar APC a Bayelsa

- Eradiri ya ce a baya bayan nan baya jin dadi a PDP sannan ga shi an bashi mukami a gwamnatin APC don yi wa kasa aiki hakan yasa dole ya sauya sheka

Tsohon kwamishinan cigaban matasa a karkashin mulkin Seriake Dickson a jihar Bayelsa, Kwamared Udengs Eradiri ya fice daga tsohuwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya koma ta All Progressives Congress (APC).

Eradiri, wanda shine tsohon shugaban kungiyar matasan Ijaw, IYC, ya koma sabuwar jam'iyyar tare da magoya bayansa fiye da 10,000 yayin taron tarbarsu da aka yi a sakatariyar jam'iyyar a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC
Bayelsa: Tsohon kwamishina da 10,000 sun fice daga PDP sun koma APC. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa

Karamin ministan albarkatun man fetur kuma jagoran jam'iyyar APC a jihar Bayelsa, Timipre Sylva ne ya tarbi wadanda suka baro PDPn suka dawo APC.

Sylva, yayin tarbar Eradiri ya bayyana dawowa jam'iyyarsa da sukayi a matsayin abin alheri.

Eradiri, wanda a yanzu shine mashawarci na musamman kan harkokin matasa ga shugaban NDDC, Akwa Effiong ya kasance sananne wurin tattara kan matasa a yankin Niger Delta.

KU KARANTA: An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

A jawabin da ya yi wurin taron, Eradiri ya ce ya fice daga tsohuwar jam'iyyarsa ya dawo APC ne saboda nadin da aka yi masa a NDDC.

Ya ce, "Na dade a PDP amma a baya bayan nan abubuwa ba su min dadi. Yanzu da gwamnatin tarayya ta kira ni don in bada gudunmawa na ga kasa, ba zai yiwu ina wata jam'iyya ba sannan in rika yi wa wata jam'iyya daban aiki. Domin samun ikon yin aiki na yadda ya dace ya zama dole in bar tsohuwar jam'iyyar."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel