Yanzu yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan kwanaki huɗu a Daura

Yanzu yanzu: Buhari ya dawo Abuja bayan kwanaki huɗu a Daura

- Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya koma fadar gwamnati ta Aso Rock a Abuja

- Shugaban kasar ya tafi mazabarsa a Daura jihar Katsina domin sabunta rajistar jam'iyya

- Shugaban kasar ya shafe kwanaki hudu a Daura inda wasu gwamnonin APC suka ziyarce shi

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dawo fadar gwamnati ta Aso Rock Villa da ke Abuja kamar yadda hadiminsa Bashir Ahmad ya sanar a Twitter.

Shugaban kasar ya tafi Daura a jihar Katsina ne mazabarsa domin sabunta rajistarsa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Ya shafe kwanaki huɗu a tafiyar.

Wasu daga cikin gwamnonin jam'iyyarsa ta APC sun yi balaguro zuwa Daura domin ganawa da shugaban ƙasar.

KU KARANTA: An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa

A cewar mai bawa shugaban kasar shawara na musamman kan kafafen watsa labarai, Mallam Garba Shehu, shugaban kasar yana mutunta aikin sabunta rajistar zaben musamman saboda demokradiyyar kasar da kuma bukatar shugabanci na gari da al'umma ke nema.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel