'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa

'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa

- Yan bindiga sun kai wa tsohon dan majalisar dokokin jihar Sokoto, Abdulwahab Goronyo hari a gidansa

- Yayin harin, sun harbi tsohon dan majalisar a kafarsa sannan sun kuma awon gaba da matarsa

- Majiya daga iyalan tsohon dan majalisar ta tabbatar da harin da aka kai masa a cikin dare

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun kai tsohon dan majalisar dokokin jihar Sokoto, Abdulwahab Yahaya Goronyo hari sun kuma yi awon gaba da matarsa.

SaharaReporters ta gano cewa an kai wa tsohon dan majalisar hari ne a gidansa da ke karamar hukumar Goronyo a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa
'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa. Hoto: @SaharaReporters
Asali: Twitter

"Yan bindiga sun kai wa Hon Abdulwahab hari a daren jiya, sun harbe shi a kafarsa sun kuma tafi da matarsa," a cewar wani majiya daga iyalensa.

Sokoto na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma a Nigeria inda yan bindiga ke adabar mutane. Masu garkuwa da mutane da yan bindiga sun dade suna kai wa al'umma hare hare.

KU KARANTA: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Gwamnatin jihar ta yi yarjejeniyar sulhu da yan bindigar a shekarar 2019.

Amma duk da hakan har yanzu ana kai wa garuruwa da dama hare hare inda a wasu lokutan ake sace mutane don karbar kudin fansa ko kuma a kashe su.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel