Na san Buhari sosai, mun yi aiki tare, amma yanzu ya sauya

Na san Buhari sosai, mun yi aiki tare, amma yanzu ya sauya

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kara sukar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, akan harkar tsaro

- A cewar Obasanjo, babban abin kunya ne ace shugaba Buhari, a matsayin tsohon soja, ya gaza magance rashin tsaro

- Obasanjo ya bayyana cewa akwai banbanci a tsakanin Buharin yanzu da tsohon Buharin da ya sani

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya soki shugaba Muhammadu Buhari akan harkar tsaron ƙasar nan.

Mr Obasanjo, ya ce, abin takaici ne yadda shugaban kasa mai matsayin babban hafsan hafsoshin kasar nan ya gaza kawo karshen yan tayar da ƙayar baya.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi wannan furuci ne jiya Lahadi da masanin tarihin nan, Toyin Falola, inda ya buƙaci shugaban ƙasa mai ci da ya farka daga dogon baccin da yake yi.

Kodayake ya nuna rashin yardarsa kan iƙirarin cewa ba shugaba ƙasar ba ne ke juya kujerar mulkin ƙasar.

KARANTA: An kama matasan da ke dillancin hotuna da bidiyon tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

“Zan iya cewa na san Shugaba Buhari saboda ya yi aiki da ni. Amma sau da yawa na kan tambayi mutane, shi ne ko kuwa ya canza ne daga Buhari da na sani? Ban yarda da maganar mutane cewa wannan Buhari daga Sudan ya ke ba, duk da wannan shirmen" in ji jaridar Premium Times.

Na san Buhari sosai, mun yi aiki tare, amma yanzu ya sauya
Na san Buhari sosai, mun yi aiki tare, amma yanzu ya sauya @Premiumtimesng
Asali: Twitter

KARANTA: Mata sun mayarwa da IGP martani mai zafi akan korar jami'ar da ta yi ciki ba tare da aure ba

Amma da abin da nake gani, na yi imani watakila zai yi tunanin abin da ya gada. Wataƙila zai ɗau darasi daga abin dake faruwa yan kwanakin nan. Idan kai babban kwamanda ne ana samun tashe tashen hankula na faruwa, to ya kamata ka farka," a cewarsa.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa Obasanjo ya yi Allah ya isa yayin da ya ke bayyana cewa yana da masaniyar cewa marigayi Umaru Musa Yar'adua bashi da koshin lafiya kafin ya goyi bayansa.

Tsohon shugaban kasar ya musanta zargin cewa kutunguila da kitimurmura suka sanya shi bawa Yar'adua takara a 2007.

Obasanjo ya jingine manyan 'yan siyasa da suka hada da tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida, da mataimakinsa a wancan lokacin, Atiku Abubakar, tare da goyawa Yar'adua baya wajen samun tikitin takara a jam'iyyar PDP.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel