An kama matasan da ke dillancin hotunan tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

An kama matasan da ke dillancin hotunan tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo

- Wasu matasa sun shiga hannu bisa zargin lalata da 'yammata tare da nadar faifan bidiyo da daukan hotuna domin sayarwa ga dillalan batsa da badala a duniya

- 'Yan sandan kasar Brazil ne suka fara ankarar da jami'an 'yan sandan Nigeria na kasa da kasa barnar da matasan ke tafkawa

- Matasan na sayar da hotuna da faifan bidiyon da suka nada ga shafin dandalin sada zumunta mallakar wani dan kasar Brazil

Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa ta kama wasu matasa 'yan Kano da ke dillancin hotunan tsiraicin mata a kafar sada zumunta.

Frank Mba, kakakin rundunar 'yan sandan Nigeria, ya ce mutanen da suka kama suna sayar da hotuna da faifan bidiyon lalata da mata a shafin WhatsApp mallakar wani dan kasar Brazil.

A cewar Mba, jami'an 'yan sanda na kasa da kasa (Interpol) da ke aiki a Abuja sune suka bi diddigi tare da kama mutanen, kamar yadda sashen Hausa na BBC ya rawaito.

KARANTA: Buhari: APC ba zata kara daurewa wani dan takara gindi daga Abuja ba

An samu kayayyaki da suka hada da manyan wayoyi guda uku da na'ura mai kwakwalwa da za'a iya dorawa a cinya.

An kama matasan da ke dillancin hotunan tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo
An kama matasan da ke dillancin hotunan tsiraicin 'yammatan Kano a yanar gizo
Asali: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa an samu hotuna da faifan bidiyo na yara mata 'yan kasa da 18 da masu laifin suka sayar a yanar gizo.

KARANTA: Mata sun mayarwa da IGP martani mai zafi akan korar jami'ar da ta yi ciki ba tare da aure ba

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar kama masu laifin ne bayan samun bayanan sirri daga rundunar 'yan sandan kasar Brazil.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa NDLEA, hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nigeria, ta samu samu nasarar kama hodar ibilis ta biliyan N30 a Legas.

Jami'an hukumar sun kama hodar ibilis din ne a wurin wata mata mai suna Onyejegbu Ifesinachi, 'yar shekaru 33 da haihuwa.

Matar ta shiga hannu ne ranar 27 ga watan Janairu a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke jihar Legas bayan dawowar ta daga kasar Brazil.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel