Mata sun tambayi IGP yaushe zai fara korar 'yan sandan da suke yi wa mata cikin shege

Mata sun tambayi IGP yaushe zai fara korar 'yan sandan da suke yi wa mata cikin shege

- A cikin makon nan ne rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanar da korar wata jami'a da ta yi cikin shege

- Tun bayan fitar da sanarwar jama'a ke cigaba da bayyana mabanbantan ra'ayi yayin da wasu suka nuna fushinsu

- Wata 'yar gwagwarmaya da ke shugabantar kungiyar mata ta tambayi babban IGP Adamu yaushe zai fara korar 'yan sanda maza da ke yi wa mata cikin shege

Shugabar wata kungiya mai rajin ganin mata sun tsaya da kafafunsu, Joe Okei-Odumakin, ta roki babban sifeton rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya kori jami'an 'yan sandan da suka taba yi wa wata mace ciki ba tare da aure ba.

Okei-Odumakin ta bayyana hakan ne yayin martani akan korar wata 'yar sanda, Olajide Omolola, saboda ta yi ciki ba tare da aure ba.

Yayin tattaunawar ta da jaridar Punch ranar Alhamis, 'yar gwagwarmayar ta bayyana korar Omolola a matsayin "zallar nuna wariya da banbancin jinsi".

KARANTA: Kura ta ci kura: An yi kazamin artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a Katsina

A cewar ta, jami'an 'yan sanda da dama, a baya da kuma har yanzu, sun yi wa dumbin mata ciki ba tare da aure ba.

Okei-Odumakin ta bukaci rundunar 'yan sanda ta fara girmama jami'anta Mata kamar yadda take girmama jami'ai Maza.

Mata sun tambayi IGP yaushe zai fara korar 'yan sandan da suke yi wa mata cikin shege
Mata sun tambayi IGP yaushe zai fara korar 'yan sandan da suke yi wa mata cikin shege
Asali: Twitter

"Babban abin takaici ne ace a wannan zamanin rundunar 'yan sanda ta nuna irin wannan halayya ta daukan mataki mai tsanani akan jami'ar 'yar sanda," a cewarta.

KARANTA: Hoton mace bakar fata zai maye gurbin na tsohon shugaban Amurka a jikin Dala

Kafafen yada labarai sun wallafa rahotannin martanin 'yan Najeriya akan korar jami'ar mai mukamin kofur.

'Yan Nigeria da dama sun bayyana mamaki da bacin ransu akan hukuncin da rundunar 'yan sanda ta zartar akan Omolola saboda kawai ta yi ciki ba tare da aure ba.

A ranar Laraba ne Legit.ng ta rawaito cewa rundunar soji ta tura rundunar dakarunta mata zalla 300 zuwa babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya jagoranci tawagar jami'an gwamnatinsa domin tarbar rundunar sojojin.

El-Rufa'i ya bayyana cewa ganin rundunar matan ya kara masa karfin gwuiwar cewa nan bada dadewa ba batun garkuwa da mutane da sauran aiyukan ta'addanci a hanyar zai kare.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng