Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari, Sarkin Musulmi da Malaman Addini

Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari, Sarkin Musulmi da Malaman Addini

- Gwamnatin tarayya ta shirya taro na musamman da Malaman addini kan rigakafin Korona

- Gwamnatin ta ce tana sa ran samun sahun farkon rigakafin a watan Febrairu

- Cutar Korona ta hallaka dubunnan mutane a Najeriya da wasu kasashen duniya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta lamuran addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar, malaman addinin Musulunci da Limamai sun amince gwamnatin Buhari na iyakan kokarinta wajen yaki da annobar COVID-19 a Najeriya.

Malaman addinin, a takardar da suka baiwa manema labarai sun bayyana cewa lallai sun amince gwamnatin tarayya za ta gwada rigakafin Korona kafin ta baiwa yan Najeriya.

Malaman addinin sun bayyana haka ne a taron da hukumar cigaban kiwon lafiya a Najeriya NPHDA ta shirya a Abuja domin fahimtar da su muhimmancin rigakafin Korona da kuma watsi da rade-raden cewa akwai na'urar leken asiri cikin rigakafin Koronan da za'a kawo Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Amma a takardar da jagororin Musulman suka rattafa hannu, sun bayyana cewa su yarda shugaba Buhari ba zai hada baki da turawa wajen kashe yan Najeriya ba.

"Idan Turawa na son cutar da Najeriya ta hanyar rigakafi ko wata hanya, da tuni zasu yi hakan ba tare da jiran wata annoba ba," wani sashen jawabin yace.

"Musulmai sun amince da gwamnatin tarayya kuma duk da cewa kungiyar lafiyan duniya WHO bata amince da rigakafin ba, wajibi ne a gwada kafin baiwa yan Najeriya."

Daga cikin wadanda suka rattafa hannu akwai sakatare janar na NSCIA, Farfesa Ishaq Oloyede; Barista Haroun Eze, Farfesa Mahmoud Eze, da Dr Faisal Shuaib.

KU KARANTA: Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu

Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari, Sarkin Musulmi da Malaman Addini
Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari, Sarkin Musulmi da Malaman Addini Hoto: Presidency
Source: Facebook

KU KARANTA: Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

A bangare guda, kwamitin hana yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya PTF na shawaran kafa dokar kulle a birnin tarayya Abuja, jihar Legas da jihar Plateau.

Mamban kwamitin, Mukhtar Muhammad, wanda ya bayyana hakan ranar Juma'a inda ya bayyana damuwar kwamitin kan yadda ake yawan kamuwa da cutar a jihohin nan uku.

Muhammad ya ce bayanai sun nuna cewa wadannan birane uku akafi kamuwa da cutar tun da annobar ta dawo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel