COVID-19: Gwamnatin tarayya na shirin saka dokan kulle a Legas, Abuja da Plateau

COVID-19: Gwamnatin tarayya na shirin saka dokan kulle a Legas, Abuja da Plateau

- Najeriya ta kafa sabuwar dokar hukunta masu saba dokokin da aka kafa don dakile yaduwar COVID-19

- A ranar Laraba, mutane 22 suka rasa rayukansu sakamakon cutar

- Adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ta zarce milyan 100

Kwamitin hana yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya PTF na shawaran kafa dokar kulle a birnin tarayya Abuja, jihar Legas da jihar Plateau.

Mamban kwamitin, Mukhtar Muhammad, wanda ya bayyana hakan ranar Juma'a inda ya bayyana damuwar kwamitin kan yadda ake yawan kamuwa da cutar a jihohin nan uku.

Muhammad ya ce bayanai sun nuna cewa wadannan birane uku akafi kamuwa da cutar tun da annobar ta dawo.

A cewar Alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC, Mutane 46,935 suka kamu a Legas, 16,470 a Abuja kuma 7,801 a Plateau, tun da cutar ta bulla a Najeriya.

Yayinda aka tambayesa kan yiwuwan saka dokar kulle, Muhammad yace: "Ko zamu saka dokar kulle, ba jiha gaba daya za'a sa ba. Makonnin baya da mukayi bincike mun gano wasu kananan hukumomi da akafi kamuwa."

"Yawanci birane ne cikin Legas, Abuja, Kaduna da Plateau."

KU KARANTA: Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)

COVID-19: Gwamnatin tarayya na shirin saka dokan kulle a Legas, Abuja da Plateau
COVID-19: Gwamnatin tarayya na shirin saka dokan kulle a Legas, Abuja da Plateau
Asali: Twitter

KU DUBA: Bayan shekaru biyar, an ceto daya daga cikin yan matan Chibok

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.

Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba. Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za'a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel