Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu

Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu

Masaniyar sinadarin abinci kuma wacce ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta rasu.

Matar 'yar kasar Indonisiya ta sha yabo daga wajen mutane a fadin duniya musamman a kasarta ta Indinosiya.

A cewar rahoton BBC, matar ta rasu tana mai shekara 59 a duniya.

@Gustirapi ya bayyana hakan a shafin Tuwita ranar Laraba, 27 ga watan Junairu, 2021.

Jawabin yace: "Yanzu mukayi rashin Mrs. Nunuk Nuraini, masaniyar sinadari wacce ta kirkiri abinda akafi sani da 'Indomie' a yau."

Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu
Matar da ta kirkiri taliyar Indomie, Nunuk Nuraini, ta mutu @gusitirapi
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng