Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

- Hafsin sojin kasa mai murabus, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ce ya gyara harkar sojoji fiye da yadda ya taras da ita

- Buratai ya yi wannan furucin ne a ranar Juma'a a Abuja yayin taron faretin saukarsa daga kujerarsa

- A cewarsa, ya yi gyara matuka kama daga walwalar soji har zuwa bayar da cikakken horarwa a garesu

Tsohon hafsin sojan kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai mai murabus, ya ce ya gyara harkar sojin Najeriya fiye da yadda ya sameta.

Ya furta hakan ne a wani taron faretin saukarsa daga kujerarsa a ranar Juma'a a Abuja, Daily Trust ta wallafa.

Ya kara da cewa ya tabbatar da cewa ya bai wa sojojin cikakkiyar horarwa da kuma inganta walwalarsu.

Kamar yadda yace "Yau ranar farinciki ce ba ta takaici ba, saboda zan yi murnar barin sojojin Najeriya fiye da yadda na same su.

KU KARANTA: Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC

Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai
Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

"Na samu nasarar ganin na yi yaki da rashin tsaro a kasar nan a lokacin ina bisa mulki.

"Mun dade muna fuskantar matsaloli na rashin kudi amma nayi kokarin ganin na yi yaki da 'yan ta'adda a kasar nan.

"Sojojin Najeriya sun dade suna yakar ta'addanci a fadin Najeriya. Kuma ina horarku da ku cigaba da ayyukan alkhairin da muka fara."

Buratai ya ce ya kamata yayi bankwana da sojoji a yanzu, kuma ya mika godiyarsa akan irin yadda sojoji suka zage damtse suka yi ayyuka tukuru wurin kawo karshen ta'addanci a kasar nan.

KU KARANTA: 2023: Wata kungiyar Musulunci ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhaammadu Buhari ya mika wasika dauke da bukatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaron da ya nada ga majalisar tarayyar kasar nan.

Kamar yadda takardar da ta samu sa hannun mai bada shawara na musamman ga shugaban kasan a kan harkokin majalisar, Babajide Omoworare ta nuna, wasikar Buhari an yi ta ne ga shugaban majalisa Ahmad Lawan dauke da kwanan wata 27 ga Janairu.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya sanar da nada sabbin hafsoshin tsaron a ranar Talatar da ta gabata, Premium Times ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel