Abacha ya wawuri kudin Najeriya lodi-lodi, Lauya a kasar Swizalan

Abacha ya wawuri kudin Najeriya lodi-lodi, Lauya a kasar Swizalan

- Shekaru 23 bayan mutuwarsa, har yanzu ana ambatar suna tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha

- Dalilin haka shine zargin wawuran biliyoyin kudi da tsohon shugaba ya boye a kasashen waje

- Wani lauyan kasar Swizalan ya ce ya kwashe shekaru 20 yana binciken kudin da Abache ya boye

Wani lauya a kasar Swizalan, Enrico Monfrini, ya ce ya kwashe shekaru 20 yana aiki domin gano kudaden da mulkin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta boye.

Channels TV ta ruwaito lauya Monfrini da cewa gwamnatin Obasanjo ce ta farko da ta tuntubesa wajen taimaka mata wajen kwato kudaden Abacha ya boye a kasashen duniya.

Ya yi bayanin cewa a binciken da ya gudanar, ya gano yadda marigayi Abacha ya karkatar da kudade bankunan kasar Swizalan lodi-lodi.

A cewarsa, kawo 2018, kudin da Abacha ya sace da aka samu nasarar dawo da su ya zarce dala bilyan 1 ($1billion)

Ya ce a farko, Abacha ya karkatar da dala bilyan hudu zuwa bilyan biyar a karon farko.

Ya kara da cewa har yanzu ana sa ran amso $30million daga Birtaniya, $144million daga Faransa, da kuma $18million daga New Jersey, USA.

KU KARANTA: Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

Abacha ya wawuri kudin Najeriya lodi-lodi, Lauya a kasar Swizalan
Abacha ya wawuri kudin Najeriya lodi-lodi, Lauya a kasar Swizalan Credit: @CFR_org
Source: Twitter

KU KARANTA: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

A bangare guda, Najeriya ta sauya lamba ta 149 cikin jerin kasashe mafi rashawa a duniya a 2020, bisa alkaluman binciken da Transparency International ta saki.

Najeriya ta samu maki 25 cikin 100. Transparency International na bada maki ne daga 0 zuwa 100. Sifiri (0) na nufin kasar da tafi rashawa, 100 kuma kasa mara rashawa.

Hakan na nufin cewa rashawa ta kara yawa a Najeriya bana da maki 29, sabanin maki 27 da Najeriya ta samu a 2018.

Bisa Alkaluman, Najeriya ta zama kasa mafi rashawa ta biyu a yammacin Afrika, yayinda kasar Guinea Bissau ta zama kasa mafi rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel