Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi rashawa a Afrika ta yamma

Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi rashawa a Afrika ta yamma

- Kamar yadda ta saba, kungiyar Transparency International jerin kasashen da akafi rashawa

- A wannan karon, rashawa ta sake muni a Najeriya da nahiyar Afrika

- Kasar Somalia da South Sudan ne kasashe biyu da aka fi rashawa a duniya

Najeriya ta sauya lamba ta 149 cikin jerin kasashe mafi rashawa a duniya a 2020, bisa alkaluman binciken da Transparency International ta saki. Najeriya ta samu maki 25 cikin 100.

Transparency International na bada maki ne daga 0 zuwa 100. Sifiri (0) na nufin kasar da tafi rashawa, 100 kuma kasa mara rashawa.

Hakan na nufin cewa rashawa ta kara yawa a Najeriya bana da maki 29, sabanin maki 27 da Najeriya ta samu a 2018.

Bisa Alkaluman, Najeriya ta zama kasa mafi rashawa ta biyu a yammacin Afrika, yayinda kasar Guinea Bissau ta zama kasa mafi rashawa.

A nahiyar Afrika, kasashe 12 kadai suka fi Najeriya rashawa. sune Zimbabwe, Chadi, Eritrea, Burundi, Congo, Guinea Bissau, DC Congo, Libya, Equatorial Guinea, Sudan, Somalia da South Sudan.

Kasar Somalia da South Sudan ne kasashe mafi fama da rashawa a duniya.

Shugaba Buhari ya zama shugaban kasa da yayi alkawarin kawar da rashawa da ta zama annoba na tsawon shekara da shekaru.

Amma tun lokacin da ya zama shugaban kasa, rashawa na kara yawa a kasar.

DUBA NAN: Bincike ya nuna wiwi zai iya rage yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19

Najeriya ta zama kasa mafi rashawa ta biyu a Afrika ta yamma
Najeriya ta zama kasa mafi rashawa ta biyu a Afrika ta yamma Hoto: Presidency
Asali: Facebook

KU KARANTA: COVID-19 ta shiga jerin kalubalen duniya kamar ta'addanci, rashawa, in ji Buhari

A bangare guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin ganawa da shugabannin hafsoshin kasar a ranar Talata ya ce gwamnatinsa ba ta samu sauki ba wajen cika alkawuran da ta dauka a shekarar 2015.

A cewar wata sanarwa da Adesina ya fitar, shugaban ya bukaci shugabannin hafsoshin da su kasance masu kishin kasa, yana mai cewa kasar na cikin yanayin neman taimakon gaggawa.

Sanarwar ta ambato Shugaban yana fadawa shugabannin hafsoshin, "Muna cikin dokar ta baci. Ku zama masu kishin kasa, ku yi wa kasar aiki da kyau, saboda amincinku ga kasar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

CREDIT: PUNCH

Asali: Legit.ng

Online view pixel