'Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun kone gidaje a rugar Fulani a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun kone gidaje a rugar Fulani a Kaduna

- Yan bindiga sun kai hari a rugar Fulani da ke kauyen Na'ikko a Kaduna

- A yayin harin sun halaka mutane 12 sun kuma kone gidaje masu yawa

- Bayan jajanta musu, kwamishinan tsaro na jihar ya yi alkwarin binciko wadanda suka kai harin

Yan bindiga sun kashe mutane goma sha biyu sannan sun kona gidaje a yayin da suka kai hari a wani rugan Fulani da ke kauyen Na'ikko a karamar hukumar Giwa na jihar Kaduna, Vanguard ta ruwaito.

Wadanda suka tsira da ransu sun tsere daga gidajensu sun tafi kauyen Barkallahu da ke karamar hukumar Igabi inda suke zaune a matsayin yan gudun hijira.

Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun kone gidaje a rugar Fulani a Kaduna
Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun kone gidaje a rugar Fulani a Kaduna. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Mista Samuel Aruwan ya ziyarci sansanin yan gudun hijirar kuma ya jajantawa wadanda abin ya shafa.

Ya yi kira gare su da 'su bari doka ta yi aikinta su guji daukan fansa."

Ya ce gwamnatin jihar, "za ta yi duk mai yiwuwa domin kama wadanda suka kai harin."

KU KARANTA: Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi

Wani da ya tsira daga harin, Malam Nura Haruna ya shaidawa kwamishinan cewa ya rasa yaransa biyu da yan uwansa biyu a harin.

A cewarsa, "yan bindigan sun zo kauyen mu suka bude mana wuta. Muna kira ga jami'an tsaro da gwamnatin jihar su binciko yan bindigan su hukunta su."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel