Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi

Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi

- Alhaji Sa'ad Abubakar II, sarkin musulmi ya koka kan yadda mafi yawancin mutane ke daukan dukkan fulani a matsayin masu laifi

- Sarkin musulmin ya ce ba adalci bane tsangwamar kabilar fulani baki dayanta duba da cewa akwai mutanen kirki da dama a cikin Fulani

- Sultan, wanda shine shugaban kwamitin amintattu na Miyetti Allah ya yi wannan jawabin ne yayin taron kungiyar a ranar Juma'a a Abuja

Sarkin Musulmi, Mai marataba Muhammadu Sa'ad Abubakar III ya soki kudin goro da ake yi wa dukkan fulani saboda hare haren da wasu mutane da ake ikirarin yan kabilar ne ke yi, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke magana yayin taro da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, MACBAN, a ranar Juma'a a Abuja 29 ga watan Janairu, Sultan wanda shine shugaban kwamitin amintattu na MACBAN, ya ce duk da cew akwai wasu fulani da ke laifi kamar yadda ake samu a wasu kabilun, ba daidai bane a rika yiwu dukkan fulani kalon bata gari.

Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi
Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Mun gwammace mu mutu da mu bari Sarkin Fulani ya dawo Oyo, in ji mutanen Igangan

A yayin da ya amince akwai fulani cikin galibin masu garkuwa da mutane, Sultan din ya ce ba su kadai suke shirya garkuwar ba domin suna samun taimakon wasu kabilun.

KU KARANTA: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima

Ya ce;

"Nima bafulatani ne amma ni mutumin kirki ne. Ni ba mai laifi bane. Wadanda ke aikata laifi suna da yawa a sasan kasar. Ba daidai bane a wari wata kabila daya ana danganta ta da wani laifi.
"Misali, idan sun karbi N10m ina zaka je ka kashe kudin a daji? Kudin cikin gari zai koma, na fada wa Sufetan Yan sanda cewa ba wai munce Fulani ba su garkuwa da mutane bane kamar yadda sakataren Miyetti Allah ya fadi, bakwai zuwa takwas cikin wadanda ake kamawa da garkuwa Fulani ne amma hakan baya nufin duk wani Fulani mai laifi ne.
"Ya zama dole mu hada hannu wuri guda don kawo karshen wannan matsalar. Za mu tuntubi shugaban kasa ya yi wa makwabtan mu na kasashen Afirka ta Yamma inda muke da Fulani kamar Senegal, Niger Republic Guinea da Mali domin mafi yawancin bata garin su kan shigo da wasu kasashen ne suyi laifi su koma."

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164