Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano

Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano

- Wata baiwar Allah ta rasu kwanaki biyar bayan daura mata aure a jihar Kano

- An daura auren Khadijat Kabir Ali Mai Katifa ne a ranar Lahadi 24 a watan Janairu

- Iyalai da yan uwa sun yi wallafa rubutu na ta'aziyyar rasuwarta tare da yi mata addu'o'i

Wata mata yar Najeriya mai suna Khadaijat Kabir Ali Mai Katifa ta riga mu gidan gaskiya kwanaki biyar bayan daura mata aure.

An daura wa Khadija aure ne da Ibrahim Dan Azumi, wani zakakurin mai goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Lahadi 24 ga watan Janairun shekarar 2021 a G/Dutse da ke jihar Kano.

DUBA WANNAN: Mun gwammace mu mutu da mu bari Sarkin Fulani ya dawo Oyo, in ji mutanen Igangan

Amarya ta rasu kwanaki 5 bayan daurin aurenta a Kano
Amarya ta rasu kwanaki 5 bayan daurin aurenta a Kano. Hoto: Muhammad Yusuf Shareef
Asali: Twitter

Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano
Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano
Asali: Facebook

A cewar wasu yan uwanta, ta rasu ne a safiyar ranar Juma'a 29 ga watan Janairun 2021.

DUBA WANNAN: Ba dukkan fulani bane masu aikata laifi, in ji Sarkin Musulmi

Ga wasu hotunan rubutun da wasu suka wallafa game da rasuwarta.

Muhammad Yusuf Shareef ya rubuta:

"Allah yajikan ki kanwata, Allah yasadaki da Annabi, ya kyautata namu zuwan Amin. Malam Abba mijinta da iyayen ta Allah ya bamu hakuri jure rashin ta Amin."

Ali Rabi'u Ali ya rubuta:

"InnalilLahi wa inna ilaiHi raji'un! Allah Ya yiwa kanwata Khadija Kabir Ali (Baby) rasuwa, Amarya ce wadda aka daura aurenta ranar lahadi 24/1/2021, za'ayi jana'izarta a Dala kofar Gidan Alhaji Rabi'u Ali Maikatifa da karfe 9:00 na safe. Allah Ya jikan ta da Rahma"

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel