Sabbin hafsoshin tsaro: NGF tayi martani, ta sanar da Buhari abu 1 da ya dace yayi

Sabbin hafsoshin tsaro: NGF tayi martani, ta sanar da Buhari abu 1 da ya dace yayi

- Kungiyar dattawan arewa (NGF) ta ce ba canja shugabannin tsaro kadai ne zai kawo karshen rashin tsaro ba a Najeriya

- Ta ce wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya tsayin-daka a matsayinsa na kwamandan shugabannin tsaron don bayar da umarni

- A cewar NGF, duk da an daina sanya bama-bamai a kasar nan yanzu, amma Boko Haram da masu garkuwa da mutane sun gama illata kasar nan

NGF ta ce ba canza shugabannin tsaro ne kadai zai kawo garanbawul ba ga matsalolin tsaron da Najeriya take fuskanta, Punch ta wallafa hakan.

Wajibi ne shugaba Muhammadu Buhari ya sanya ido kuma ya dinga bai wa shugabannin tsaro umarni yadda ya dace a matsayinsa na kwamandansu.

"Babban matakin da Buhari zai dauka shine canja salo da kuma fuskantar matsalolin tsaro gadan-gadan. Sai ka ji yana cewa ya taras da tabarbarewar tsaron Najeriya a 2015 ya nunka halin da ake ciki yanzu, wannan kalaman suna matukar tayar da hankali.

Sabbin hafsoshin tsaro: NGF tayi martani, ta sanar da Buhari abu 1 da ya dace yayi
Sabbin hafsoshin tsaro: NGF tayi martani, ta sanar da Buhari abu 1 da ya dace yayi. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Marasa rinjayen majalisar dattawa sun mika bukata 1 ga sabbin hafsoshin tsaro

"Tabbas an daina sanya bama-bamai a Najeriya, amma 'yan Boko Haram sun riga sun kashe mutane masu yawa marasa adadi, ba za mu cigaba da lamuntar hakan ba," Yace.

Kakakin NGF, Dr Hakeem Baba-Ahmed a ranar Laraba yayin da Channels ta ke tattaunawa dashi ya fadi hakan. A cewarsa arewa maso gabas tana cikin wani hali wanda take bukatar dauki daga shugabannin tsaro.

A cewar Baba-Ahmed, ba nadin kadai ne zai kawo canji ba, ana fatan ya dauki matakin ne ba don surutun jama'a ba, sai don kawo karshen tashin hankali, rikici da rashin tsaro da kasarnan take fuskanta.

KU KARANTA: Bidiyon magidanci yana tozarta matarsa da ya kama da kaninsa suna cin amanarsa

A wani labari na daban, a ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin hafsoshin tsaron kasar nan da suka kasance a ofishinsu tun 2015 da wasu sabbin, The Cable ta wallafa.

Kafin daukar wannan matakin, jama'a da dama sun dinga kira ga shugaban kasar da ya sallami hafsoshin tsaron sakamakon hauhawar rashin tsaro a fadin kasar nan.

A yayin da shugaban kasan ya nada sabbin hafsoshin tsaron, 'yan Najeriya sun dinga bayyana ra'ayoyinsu a Twitter da yadda suke ji game da wannan cigaban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel