A bar sabbin jini su yi aiki, 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon nadin Buhari

A bar sabbin jini su yi aiki, 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon nadin Buhari

- Sakamakon hauhawar rashin tsaro a kasar nan, jama'a sun dinga kira ga Buhari da ya sallami hafsoshin tsaro

- Nadin sabbin hafsoshin tsaron a ranar Talata ya sa 'yan Najeriya suka dinga maganganu kala-kala

- Wasu na rokon sabbin shugabannin tsaron da su dage yayin da wasu ke ganin cewa an makara a kan tsaron kasar

A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya maye gurbin hafsoshin tsaron kasar nan da suka kasance a ofishinsu tun 2015 da wasu sabbin, The Cable ta wallafa.

Kafin daukar wannan matakin, jama'a da dama sun dinga kira ga shugaban kasar da ya sallami hafsoshin tsaron sakamakon hauhawar rashin tsaro a fadin kasar nan.

A yayin da shugaban kasan ya nada sabbin hafsoshin tsaron, 'yan Najeriya sun dinga bayyana ra'ayoyinsu a Twitter da yadda suke ji game da wannan cigaban.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin kwace kudaden bankunan tsohon gwamnan Zamfara

A bar sabbin jini su yi aiki, 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon nafin Buhari
A bar sabbin jini su yi aiki, 'Yan Najeriya sun yi martani a kan sabon nafin Buhari. Hoto daga ChannelsTV.com
Asali: UGC

Ga wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a dangane da sabbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada:

KU KARANTA: Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa a ranar Talaa ta ce abinda yasa aka sallami hafsoshin tsaro a yau ba saboda sun gaza bane. Ta kara da cewa an yi hakan ne a wannan lokacin domin kara karfi a fannin yaki da ta'addanci tare da shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan.

Femi Adesina, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da Channels TV a kan siyasa kuma Punch ta kiyaye.

"Abinda yasa suka tafiya a yau ba yana nufin sun gaza bane. A gaskiya ba hakan bane. Kawai ana son sabbin jini ne da kuma sabbin dabarun yaki a kasar nan," yace yayin da yake sanar da jinjinar da Buhari yayi wa tsoffin shugabannin tsaron.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel