Bidiyon magidanci yana tozarta matarsa da ya kama da kaninsa suna cin amanarsa

Bidiyon magidanci yana tozarta matarsa da ya kama da kaninsa suna cin amanarsa

- Wani bidiyo da ke yawo a kafar sada zumunta ya nuna yadda miji ya tozarta matarsa maci amana

- Magidancin ya jira ranar zagayowar haihuwar matar sannan ya sanar da ita cewa ya san boyayyen sirrinta

- Fusataccen magidancin ya bai wa matarsa mamaki inda yayi bidiyo yana bayyana cin amanarta

Wani fusataccen magidanci ya je kafar sada zumuntar zamani domin daukar fansa daga matarsa wacce ke cin amanarsa da kaninshi.

Kamar yadda Bidiyon ya nuna, mijin ya kama matarsa da kaninsa suna cin amanarsa amma ya hakura har zuwa ranar zagayowar haihuwarsa domin ya tozarta su.

A bidiyon, an ga kyakyawar matar sanye da wata hula mai yanayin bututu. A takardar da ke hannun ta an yi rubutu da ke nuna halin da ake ciki.

KU KARANTA: Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40

Bidiyon magidanci yana tozarta matarsa da ya kama da kaninsa suna cin amanarsa
Bidiyon magidanci yana tozarta matarsa da ya kama da kaninsa suna cin amanarsa. Hoto daga @lailaijeoma
Asali: Instagram

Wani matashi wanda shine kanin magidancin yana rike da takarda wacce rubutun jikinta ke nuna cewa yayansa ya kama shi da matarsa suna lalata a wurin wanki.

Magidancin ya kara da tattara wa matarsa komatsanta a akwati sannan ya dora mata kek tare da umartarta da ta bar gidansa.

KU KARANTA: Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata

A wani labari na daban, an saka 'yan majalisar jihar Kogi gaba da caccaka bayan zagayen jihohi da suka yi suna nemawa gwamna Yahaya Bello goyon baya daga jama'a domin fitowa takarar shugaban kasa a 2023.

Yan majalisar da suka ziyarci Filato, Ebonyi da jihar Kogi, sun yi kira ga takwarorinsu da su goyi bayan Gwamna Bello idan 2023 ta iso.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, tunda har yanzu arewa ta tsakiya bata fitar da dan takarar shugaban kasa ba, akwai bukatar APC ta mika tikitinta ga Bello domin yayi takarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel