Marasa rinjayen majalisar dattawa sun mika bukata 1 ga sabbin hafsoshin tsaro
- Marasa rinjaye na majalisar dattawan kasar nan sun nuna gamsuwarsa da sauya hafsoshin tsaro
- Shugaban marasa rinjayen, Sanata Abaribe ya ce daukin da aka kawowa tsaron kasar yafi babu
- Sanata Abaribe ya yi fatan sabbin hafsoshin tsaron za su kawo sauyi a kan matsalar tsaron
Marasa rinjaye na majalisar dattawa sun nuna gamsuwarsu a kan sabon nadin sabbin hafsoshin sojin da aka samu a kasar nan.
Sun nuna sakankancewarsu da cewa za a samu sauyi a bangaren tsaron kasar nan, Daily Trust ta wallafa.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan, Enyinnaya Abaribe a martaninsa, ya ce duk da majalisar dattawa ta dinga kira ga shugaban kasa a kan sallamar hafsoshin tsaron kasar nan tuntuni, daukin da aka kawowa kasar nan a yanzu yafi babu.
KU KARANTA: Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata
Mun dade muna kira a kan sauya shugabannin tsaro. Muna fatan wadannan za su shawo kan matsalar tsaron kasar nan," Sanata Abaribe yace.
KU KARANTA: Sabbin hafsoshin tsaro: An riga an gama aika-aika ga tsaron kasa, PDP
A wani labari na daban, Nura Walwala Magaji kafinta ne mai shekaru 36 daga gundumar Zango ta karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi.
Ya ce yana alfahari da yadda ya haifa yara 13, maza 10 sai mata 3. Yana fatan cika burinsa na yarinta inda yake son haifar 'ya'ya a kalla 40.
Kamar yadda jaridar Community Vanguard ta wallafa, Magaji yana da mata hudu kuma kowacce ta haihu a cikin makonni uku. Ya ce kula da su ba zai zama matsala ba domin Allah ne ke kula da yara.
A yayin zantawa da jaridar Leadership, ya ce, "'Ya'ya kyauta ne daga Allah kuma ina farin ciki saboda matana sun haihu a cikin makonni uku. Maza uku, mace daya."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng