An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu

An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu

- Gwamnatin kasar Sin ta fara yiwa mazauna Beijing gwajin Korona ta dubura

- Ana bukatar tura auduga cikin duburan mutum na tsawon inci daya

- Za'a juya audugar ciki akalla sau biyu cikin dakikai 10 sannan a cire

- Masana sun bayyana cewa gwaji ta wannan hanyan ya fi bada sakamako na kwarai

Kasar Sin ta fara yiwa al'ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi bada sakamako na kwarai, Daily Mail ta ruwaito.

Domin yin wannan gwaji, ana bukatar tura audugar cikin dubura na tsawon inci daya zuwa biyu kuma a juyashi.

Bayan yin haka sau biyu, za'a cire audugar sannan ayi gwaji.

Mahukunta a birnin Beijing sun fara wannan gwajin ne bayan kamuwar da wani yaro dan shekara 9 yayi da cutar Korona makon da ya gabata.

Wani masani a asibitin You'an dake Beijing, Li Tongzeng, yayin hira da tashar CCTV ranar Asabar, yace an gano kwayoyin cutar Korona sun fi dadewa cikiin dubura fiye da baki da hanci.

"Mun samu cewa wasu masu cutar Korona da basu nuna alamu suna warkewa da wuri. Akwai yiwuwan ba za'a samu cutar a makogwaronsu ba cikin kwanaki uku zuwa biyar," Li ya bayyana.

"Amma cutar ta fi dadewa a samfurin da aka dauka na ba hayan mutum, idan aka hada da wadanda aka dauka daga wuraren irinsu baki, hanci da makogwaro."

KU DUBA: Sojoji a bariki na farin ciki da shewa yayinda suka samun labarin sallaman Buratai da sauran hafsoshin tsaro

An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu
An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu AFP/Getty Images
Asali: UGC

KU KARANTA: Jerin gwamnonin Najeriya 11 da suka kamu da cutar Coronavirus

A bangare guda, a ranar Talata, 27 ga watan Junairu 2021, Mutane 1,303 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 542 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 103 a Plateau da 22 a jihar Kwara.

Abin takaici, mutane 15 sun rasa rayukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel