Cutar COVID-19: Mutane 15 sun mutu, 1,303 sun kamu ranar Talata
- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara
- Kusan makonni uku a jere, yan Najeriya sama da 1000 ke kamuwa da Korona kullum
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita idan adadin ya cigaba da karuwa
A ranar Talata, 27 ga watan Junairu 2021, Mutane 1,303 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Daga cikin wadanda aka sallama, akwai mutane 542 da sukayi jinya cikin gidajensu a Legas, 103 a Plateau da 22 a jihar Kwara.
Abin takaici, mutane 15 sun rasa rayukansu.
Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 124,299 a Najeriya.
Daga cikin mutanen da suka kamu, an sallami 99,276 yayinda 1,522 suka rigamu gidan gaskiya.
KU DUBA: Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti
KU KARANTA: Wani dan kasuwa ya maka surukinsa a kotu a kan N69,000
A makon nan gwamnatin tarayya ta bada umarni ga wasu ma’aikatanta su tsaya a gidajensu, su cigaba da aiki daga can, ba tare da sai sun zo ofis ba.
Jaridar The Cable ta ce wannan umarni ya zo ne a wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta yi ta bakin shugaban ma’aikatan kasar, Folasade Yemi-Esan.
Misis Folasade Yemi-Esan ta fitar da takarda inda ta aika wa fadar shugaban kasa, majalisar tarayya, da kuma sakatarorin din-din-din na ma’aikatu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng