Sojoji a bariki na farin ciki da shewa yayinda suka samun labarin sallaman Buratai da sauran hafsoshin tsaro

Sojoji a bariki na farin ciki da shewa yayinda suka samun labarin sallaman Buratai da sauran hafsoshin tsaro

Jami'an sojojin Najeriya a barikinsu sun cika da farin ciki yayinda suka samu lamarin sallaman tsaffin hafsoshin tsaro a ranar Talata da kuma sanar da wadanda zasu maye gurbinsu.

Wani bidiyon dakikai 20 ya nuna lokacin da wasu Sojojin ruwa a barikinsu da ake kyautata zato na birnin tarayya suke iwu suna rawa kan labarin.

SaharaReporters ta ruwaito cewa irin haka ya faru a sauran barikin sojoji dake fadin tarayya.

Sojoji a bariki na farin ciki da shewa yayinda suka samun labarin sallaman Buratai da sauran hafsoshin tsaro
Sojoji a bariki na farin ciki da shewa yayinda suka samun labarin sallaman Buratai da sauran hafsoshin tsaro Hoto: saharareporters.com
Source: UGC

Kalli bidiyoyin:

Bayan kiraye-kiraye daga yan majalisun tarayya da manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka yiwa shugaba Buhari ya sallami hafsoshin tsaro kuma ya nada wasu, Buhari ya amsa a yau.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita. A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel